Tsoffin abokan aiki, abokai da makusantan Marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar (mai ritaya) sun yi kira ga gwamnati da ta gaggauta sake fasali...
Tsoffin abokan aiki, abokai da makusantan Marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar (mai ritaya) sun yi kira ga gwamnati da ta gaggauta sake fasalin tsarin tsaron Nijeriya, bayan mutuwarsa a hannun ’yan bindiga, suna mai cewa lamarin ya sake bayyana irin mummunar matsalar tsaro da ƙasar ke fuskanta.
A wani taron manema labarai da suka gudanar a ranar Alhamis, ƙungiyar ta bayyana alhininta kan rasuwar tsohon babban hafsan soja, wanda aka yi garkuwa da shi tare da matarsa, Hajiya Amina Rabe Abubakar, a yankin Matazu da ke Jihar Katsina. Duk da cewa an samu nasarar ceto matarsa daga hannun masu garkuwar, Janar Abubakar ya rasu ne yayin da yake tsare a hannunsu.
Tawagar, wadda ta samu wakilcin Birgediya Janar Isma’ila Abdullahi (mai ritaya), Ambasada A. Mohammed Musawa da Air Commodore Yusuf Anas (mai ritaya), ta bayyana marigayin a matsayin jajirtaccen jami’in soja wanda ya yi fice wajen biyayya ga ƙasa, gaskiya da sadaukar da kai wajen yi wa Nijeriya hidima.
Sun yaba da ƙoƙarin da Gwamnatin Tarayya da kuma Gwamnatin Jihar Katsina suka yi wajen ganin an kuɓutar da matarsa, tare da jinjinawa shugaban ƙasa bisa yin Allah wadai da kisan da kuma sake jaddada aniyar gwamnatinsa na yaƙar ta’addanci da satar mutane.
Sai dai sun ce mutuwar Janar Abubakar ta sake fito da babbar matsalar tsaro da ta mamaye ƙasar, inda ’yan Nijeriya da dama ke rayuwa cikin fargabar hare-haren ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata ta’addanci.
A cewarsu, yawaitar sace mutane, ciki har da ɗalibai, ta zama wata babbar masifa da ke ci gaba da raunana amincewar jama’a ga ikon gwamnati na kare rayuka da dukiyoyi. Sun ƙara da cewa matsalar tsaro ta bazu a sassan ƙasar har ta kai ga cewa ya zama da wuya a bambance yankunan da ake fama da rikici da waɗanda ake ganin suna cikin zaman lafiya.
Masu jawabin sun yi kira ga ’yan Nijeriya da su guji mayar da matsalar tsaro ta zama batun siyasa ko na ƙabila da yanki, suna mai jaddada cewa ta’addanci, fashi da makami da sace mutane matsaloli ne na ƙasa baki ɗaya da ke buƙatar haɗin kai da nazari mai zurfi.
Sun yi zargin cewa gwamnatoci daban-daban sun kasa magance matsalar yadda ya kamata saboda gazawar aiwatar da manufofi, rashin haɗin gwiwa tsakanin hukumomi da kuma ƙarancin ƙudurin siyasa.
Saboda haka, sun buƙaci a ƙarfafa hukumomin tsaro, a ƙara musu kuɗaɗen gudanar da aiki da kuma ɗaukar matakan da suka fi inganci wajen yaƙi da masu tayar da ƙayar baya da sauran miyagu.
Duk da cewa sun yi maraba da haɗin gwiwar tsaro da Najeriya ke yi da ƙasashen duniya, ciki har da Amurka, sun jaddada cewa alhakin kare ƙasar ya rataya ne a wuyan Nijeriya.
“Babu wata ƙasa da za ta kare mana ƙasarmu. Taimakon ƙasashen waje zai iya zama kari ne kawai, ba zai maye gurbin ingantaccen tsarin tsaron ƙasa ba,” inji su.
Har ila yau, sun buƙaci a ƙarfafa tsaron kan iyakoki tare da haɓaka haɗin gwiwa da maƙwabtan ƙasashe irin su Jamhuriyar Nijar, Chadi da Kamaru, domin daƙile shigowar makamai ba bisa ƙa’ida ba waɗanda ke rura wutar ta’addanci da ’yan bindiga.
Dangane da kiraye-kirayen da ake yi na a bai wa fararen hula damar ɗaukar makamai domin kare kansu, sun yi kira da a yi taka-tsantsan, suna mai cewa duk wata irin manufa dole ne ta kasance ƙarƙashin tsauraran dokoki domin kauce wa yaɗuwar makamai a tsakanin jama’a.
Sun kuma buƙaci gwamnonin jihohin Arewa 19 da su samar da manufa guda ta tsaro da za ta haɗa yankin baki ɗaya wajen yaƙi da mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba, ta’addanci, ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane.
Suna kawo misalai daga ƙasashen duniya, sun nuna yadda gwamnatocin Italiya da Sri Lanka suka nuna ƙwazo da ƙudurin siyasa wajen murƙushe ƙungiyoyin ta’addanci, suna mai kira ga shugabannin Nijeriya da su nuna irin wannan jajircewa.
Haka kuma sun roƙi gwamnati da ta samar da tallafi cikin gaggawa ga iyalan jami’an tsaro masu aiki da waɗanda suka yi ritaya idan suka mutu yayin aiki ko suka fada hannun masu garkuwa da mutane da ’yan ta’adda.
Sun kuma yi kira da a ƙara ƙaimi wajen kuɓutar da dukkan ’yan Nijeriya da ke tsare a hannun masu garkuwa da mutane tare da ci gaba da ɗaukar matakan kawo ƙarshen ta’addanci, ’yan bindiga da sace-sacen mutane a faɗin ƙasar.
Mutuwar Janar Rabe Abubakar ta haifar da damuwa a sassa daban-daban na ƙasar, inda mutane da dama ke kallon lamarin a matsayin wata ƙara tunatarwa game da ƙalubalen tsaro da har yanzu ke addabar Nijeriya.

No comments