Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Juma’a a matsayin ranar hutu ga ma’aikata domin bikin cika shekaru 27 da Nijeriya take gudanar da mulkin d...
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Juma’a a matsayin ranar hutu ga ma’aikata domin bikin cika shekaru 27 da Nijeriya take gudanar da mulkin dimokiraɗiyya ba tare da katsewa ba.
Babbar Sakatare a Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Magdalene Ajani, ita ta bayyana haka cikin takardar manema labarai da ta rattaba wa hannu a ranar Alhamis a Abuja.
Ajani ta ce Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, shi ne ya ba da sanarwar hutun a madadin Gwamnatin Tarayya.
Tunji-Ojo ya sake jaddada aniyar gwamnati na kare da kuma bunƙasa ƙa’idojin dimokiraɗiyya, ciki har da bin doka da oda, gaskiya da riƙon amana, ɗaukar nauyi, da kuma shugabanci mai haɗa kowa da kowa.
Ya tabbatar da cewa Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro da abin ya shafa, za su ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da tsaro da kuma ƙarfafa zaman lafiyar cikin gida a Nijeriya.
Ministan ya bayyana cewa samun yanayi mai cike da tsaro da kwanciyar hankali yana da matuƙar muhimmanci domin dimokiraɗiyya ta bunƙasa tare da tabbatar da cigaban ƙasa mai ɗorewa.
Ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su yi amfani da wannan ranar hutun wajen yin nazari kan matsayin su na ‘yan ƙasa tare da sabunta jajircewar su wajen kare kyawawan ɗabi’u da ƙimomin ƙasa.
Ya ce, “Yayin da muke bikin wannan rana mai tarihi, muna kira ga kowane ɗan Nijeriya da ya kasance mai bin doka, ya mutunta cibiyoyin da ke ɗorewar dimokiraɗiyyar mu, tare da tuna cewa ƙarfin kowace dimokiraɗiyya yana ta’allaƙa ne ga halaye da ɗabi’un ‘yan ƙasar ta.”
Tunji-Ojo ya ƙara da cewa ranar 12 ga Yuni tana da muhimmin matsayi a tarihin Nijeriya, domin tana girmama jarumtaka, juriya da sadaukarwar waɗanda suka bayar da gudunmawa wajen kafa mulkin dimokiraɗiyya a ƙasar nan.
“Har yanzu abin da muka gada daga gare su yana ci gaba da zama abin koyi wajen tsara ƙimomi da nauyin da ya rataya a wuyan ƙasar Nijeriya,” inji shi.

No comments