Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wajen ƙaddamar da cikakken aikin gina Titin Arteria...
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wajen ƙaddamar da cikakken aikin gina Titin Arterial Road N5 (Obafemi Awolowo Way), wanda ya haɗa mahadar Life Camp da Ring Road III a yankin Dape da ke Babban Birnin Tarayya Abuja.
A yayin taron ƙaddamarwar da aka gudanar a Abuja, Sanata Shettima ya isar da saƙon Shugaba Tinubu, inda ya jaddada cewa gwamnatin tarayya ta himmatu wajen bunƙasa Abuja domin ta zama babban birni da zai dace da yawan al’ummar Nijeriya, burin tattalin arziƙinta da kuma martabar ƙasa.
Ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Tinubu za ta ci gaba da bai wa ayyukan more rayuwa muhimmanci, domin inganta hanyoyin sufuri da zirga-zirga a babban birnin tarayya.
Mataimakin Shugaban Ƙasar ya ƙara da cewa kammala wannan muhimmin aikin titi zai taimaka wajen rage tsadar jigilar kayayyaki, ƙarfafa zuba jari, da kuma samar da guraben ayyukan yi ga al’umma.
Ya ce gwamnatin tarayya na ci gaba da aiwatar da manyan ayyukan ci gaba a sassa daban-daban na ƙasar nan, domin inganta rayuwar jama'a da bunƙasa tattalin arziƙin Nijeriya.












No comments