Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Dalilan Da Ya Sa Ake Ganin Makiyaya A Cikin Birnin Abuja Suna Kiwo -Minista

Ministan bunƙasa kiwon dabbobi, Idi Muktar Maiha ya bayyana dalilin da ya sa ake ganin makiyaya na yawon kiwo a birnin Abuja, inda ya ce, ...

Ministan bunƙasa kiwon dabbobi, Idi Muktar Maiha ya bayyana dalilin da ya sa ake ganin makiyaya na yawon kiwo a birnin Abuja, inda ya ce, "Dalilan da ya sa ake ganin makiyaya a cikin birnin Abuja suna gararamba shi ne: kafin a ƙirƙiri Abuja, a wancan lokaci kusan dazukan a nan da dama wuraren kiyon dabbobi ne.

"To, bayan da aka ƙirkiri Abuja, an tanadi wurare da aka tsara jama'a za su zauna, tare da wuraren ofisoshi da wuraren gina kasuwanni da sauran wuraren more rayuwa, amma aka manta a keɓe tare da inganta inda dabbobi za su yi kiwo.

"Akwai gandun daji guda huɗu da faɗin su ya kai hekta 33 a Abuja da aka ware tun da, sannan tun da aka ware waɗannan gandun dajin a wancan lokacin da aka kirkiri Abuja, ba a taɓa yin wani abu na inganta wurin ta yadda za a maida makiyaya wurin ba.

"Tun bayan kafa ma’aikatar kula da bunƙasa kiyon dabbobi kusan shekara biyu da suka wuce, ma’aikatar ta kulla alaƙa tare da Hukumar Gudanar da Babban Birnin Tarayya ta yadda za a inganta waɗannan wurare da ke yankunan ƙauyen Kau, Karshi da sauran wurare da ke Abuja.

"Muna aiki tare da masu ruwa da tsaki wajen inganta waɗannan gandun dajin, sannan a duba yiwuwar maida makiyaya wurin sannu a hankali."

— Idi Muktar Maiha, Ministan Bunƙasa Kiyon Dabbobi, ya bayyana hakan ne a yayin taron manema labarai na Ranar Dimokuraɗiyya ta 2026 da aka gudanar a ranar Talata, 9 ga Yuni, 2026.
 

No comments