Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kamo Mata Ɗan Takarar Gwamnan Bauchi Na NDC, Ibrahim Kashim

Daga Khalid Idris Doya  Babbar Kotun Majistare da ke zama a Jihar Bauchi ta bada umurnin a kamo (bench warrant) ɗan takarar gwamna na jam’iy...

Daga Khalid Idris Doya 

Babbar Kotun Majistare da ke zama a Jihar Bauchi ta bada umurnin a kamo (bench warrant) ɗan takarar gwamna na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) a jihar Bauchi kuma tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar, Barrista Ibrahim Kashim Muhammad.

Babban Majistare 1, Abdulmumini Adamu, shi ne ya bada wannan umarni a ranar Talata 9 ga watan Yuni kan shari’a mai lamba CMCBH/870/2026, wadda Barrista Ahmed Sani da Barrista Hussaini Saraki suka shigar a kan Ibrahim Kashim suna zarginsa da ɓata musu kima da mutunci.

A cewar umarnin kotun, an bayar da sammacin ne bayan lauya mai wakiltar masu ƙara, S.U. Sarki Esq., ya nemi a kama wanda ake ƙara domin tilasta masa halartar kotu.

Kotun ta  ce, "Bayan sauraron roƙon da lauya mai wakiltar masu ƙara ya gabatar yana neman a bayar da sammacin kama wanda ake ƙara domin tilasta masa halartar kotu, tare da sauraron hujjoji da dalilan da aka gabatar, kotu ta bayar da umarnin a kama wanda ake ƙara a wannan shari’a. Idan aka kama shi, a kawo shi gaban wannan kotu mai daraja.”

Daga nan ne aka ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 23 ga Yuni, 2026 da neman a kawo mata ɗan takarar gwamnan a wannan ranar.

Asalin shari’ar da Lauyoyin biyu suka shigar kan wanda suke ƙara wanda shi ma Lauya ne. 

A cewar ƙorafin da aka gabatar gaban kotun, masu ƙarar, waɗanda dukkansu lauyoyi ne, sun kai ziyara shalkwatar Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC) da ke Abuja a watan Nuwamba, 2025, yayin da suke wakiltar tsohon kwamishinan kuɗi na Jihar Bauchi kuma ɗan takarar gwamna na jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM), Dakta Yakubu Adamu, a wasu batutuwa da suka shafi hukumar.

Masu ƙarar sun yi zargin cewa Ibrahim Kashim ma yana nan a ofishin EFCC a lokacin kuma ya gana da su tare har ma suka gaisa.

Shari’ar ta samo asali ne daga wasu kalamai da ake zargin Ibrahim Muhammad Kashim ya furta yayin wata hira kai tsaye da tashar 'Zamani TV', wata kafar yaɗa labarai ta yanar gizo, a ranar 3 ga Yuni, 2026. An gudanar da hirar ne cikin harshen Hausa kuma aka watsa ta ga masu kallo a cikin da wajen Jihar Bauchi.

A cewar takardun kotu, Kashim ya ambaci Barrista Hussaini Saraki da sunansa kai tsaye, sannan ya yi magana kan wani lauya da ya ce ya san shi da kansa amma bai ambaci sunansa ba.

Masu ƙarar sun yi zargin cewa Kashim ya bayyana a yayin hirar cewa ɗaya daga cikin lauyoyin an zarge shi kwanan nan da karɓar kuɗi daga wani abokin hulɗar kasuwanci ba tare da aiwatar da aikin da aka ba shi domin ya yi ba duk da ya amshi kuɗin. Haka kuma, an ce ya nuna yiwuwar cewa lauyoyin suna cikin waɗanda suka sanar da jami’an gwamnatin Bauchi game da ziyararsa zuwa EFCC.

Masu ƙarar sun bayyana cewa waɗannan kalamai ƙarya ne, cike da mugunta kuma na ɓata suna, suna mai jaddada cewa ba su taɓa sanar da wani jami’in gwamnati game da ziyarar Kashim zuwa EFCC ba.

Sun ƙara da cewa kalaman sun jawo musu ba’a da raini a idon jama’a, sun lalata martabarsu ta ƙwararru, kuma sun sa mutane suka fara shakkar gaskiyarsu da ƙwarewarsu a aikin lauya.

A cewarsu, kalaman sun nuna su a matsayin marasa gaskiya, marasa amana kuma waɗanda ba su cancanci amincewar abokan hulda da jama’a ba.

Saboda haka, sun tuhumi Kashim da aikata laifukan ɓata suna (Defamation) ƙarƙashin Sashe na 387 da kuma Yaɗa Ƙarya Mai Cutarwa (Injurious Falsehood) ƙarƙashin Sashe na 388 na Dokar Penal Code ta Jihar Bauchi ta shekarar 2022.

A cikin ƙorafinsu, sun roƙi kotu idan aka tabbatar da zarge-zargen, kuma aka same shi da laifi a hukunta shi bisa ga doka.

Da ya ke mayar da martani ga lamarin yayin tattaunawa da wakilinmu, Barrista Ibrahim Muhammad Kashim ya musanta cewa ya yi ƙoƙarin guje wa zaman kotu, yana mai bayanin cewa ya riga ya shirya tafi Abuja kafin a ba shi sammacin.

Ya ce: "Muna son mu fayyace wa al'umma cewa sammacin kotu da ake magana a kai an kawo shi ne a ranar Lahadi, a daidai lokacin da na riga na kammala shirye-shiryen tafiya zuwa Abuja domin wasu muhimman ayyuka da aka tsara tun da farko.

"Da samun labarin shari'ar, nan take na umurci lauyana da ya wakilce ni a gaban kotun tare da roƙon a ba mu wani sabon lokaci domin mu samu damar halarta da kuma kare kanmu yadda doka ta tanada. Saboda haka, ba daidai ba ne a fassara rashin halartar da cewa mun guje wa kotu ko kuma muna ƙin amsa gayyatar da aka yi mana.

"Muna da cikakken girmamawa ga kotuna da tsarin shari'a, kuma a shirye muke mu kare kanmu bisa doka. Ba mu ci mutuncin kowa ba, kuma ba mu aikata wani laifi da zai hana mu bayyana gaskiya a gaban kotu. 

"In sha Allah, za mu halarci kotu a lokacin da aka tsara domin ci gaba da sauraron shari'ar, kuma muna da yakinin cewa gaskiya za ta bayyana," Kashim Ibrahim ya tabbatar.


 

No comments