Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana cewa manyan ayyukan gine-gine da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta aiwata...
Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana cewa manyan ayyukan gine-gine da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar a Abuja sun kammala kuma sun shirya domin ƙaddamarwa, yayin da ake shirin bikin cika shekaru uku na mulkin sa.
Wike ya bayyana hakan ne yayin duba wasu muhimman ayyuka a Abuja, inda ya ce gwamnatin Tinubu ta nuna ƙudirin gaske wajen sauya fasalin babban birnin ƙasa ta hanyar inganta hanyoyi, gadoji da sauran ababen more rayuwa.
A cewarsa, dukkanin ayyukan da aka duba sun kai matakin kammalawa da ya kai kashi 100 cikin 100, yana mai cewa hakan hujja ce ta cewa an kawo ci gaba mai ma’ana ga al’umma.
Daga cikin ayyukan da aka duba akwai gadar Jahi–Gwarimpa, hanyar filin jirgin sama zuwa Kuje, hanyar Kuje zuwa Gwagwalada, titunan Outer Southern Expressway, da kuma gyaran ƙofar shiga birnin Abuja (Abuja City Gate).
Wike ya bayyana jin daɗinsa kan ingancin aikin da kamfanonin kwangila suka yi, inda ya ce ayyukan za su inganta zirga-zirga tare da rage cunkoso da wahalar tafiya a birnin Abuja da kewayenta.
Ya ce musamman hanyoyin Airport zuwa Kuje da Kuje zuwa Gwagwalada sun rage tsawon lokacin tafiya tsakanin birni da yankunan da ke kewayen Abuja, abin da ya ce ya inganta rayuwar mazauna sosai.
Ministan ya kuma yaba da gyaran da aka yi wa Abuja City Gate, yana mai cewa hakan zai ƙara wa birnin Abuja martaba a idon duniya a matsayin babban birni na zamani.
Ya ƙara da cewa ana shirin fara kaddamar da ayyukan a mako mai zuwa, inda ya ce shugabannin gwamnati daban-daban za su wakilci Shugaba Tinubu wajen buɗe wasu daga cikin ayyukan.
Wike ya kuma yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su taimaka wajen bayyana irin ci gaban da ake samu a FCT, yana mai cewa abin da ake yi a Abuja yana nuna yadda gwamnati ke kawo sauyi ga rayuwar al’umma.
A cewarsa, an kuma shirya fara wasu sabbin ayyukan hanyoyi a nan gaba domin ci gaba da bunƙasa ababen more rayuwa a babban birnin tarayya.






No comments