Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

ADC A Nasarawa Ta Kafa Kwamitin Sasanta 'Yan Takarar Da Suka Faɗi A Zaben Fidda Gwani

Daga Zubairu Lawal, Lafia  A wani yunƙuri na samar da haɗin kai mai ɗorewa, Jam'iyyar ADC ta samar da wani kwamitin da zai gana da '...

Daga Zubairu Lawal, Lafia 

A wani yunƙuri na samar da haɗin kai mai ɗorewa, Jam'iyyar ADC ta samar da wani kwamitin da zai gana da 'yan takarar da duka faɗi Zaben fidda gwani a faɗin jihar. An kafa kwamitin ne a ranar Talata a sakatariyar Jam'iyyar ADC da ke garin Lafia.

Jam'iyyar, reshen Jihar Nasarawa, ta kafa tare da rantsar da Kwamitin sasantawar domin duba ƙorafe-ƙorafe da rashin jin daɗin da suka taso bayan kammala zaɓen fidda gwani na jam'iyyar.

A ƙarƙashin jagorancin Shugaban Jam'iyyar na Jiha, Cif John Mike Abdul, an kafa kwamitin ne domin tattaunawa da masu neman takarar gwamna, Majalissun Dattijai, Wakilai na Tarayya da na Dokokin, waɗanda ke da koke ko rashin gamsuwa da sakamakon zaɓen fidda gwani.

An ba kwamitin wa'adin kwanaki 14 domin sasanta mambobi tare da gabatar da rahotonsa nan da nan bayan kammala aikinsa.

A jawabin sa na ƙaddamarwa, Shugaban Jam'iyyar ADC Cif Mike ya ce an ɗora wa kwamitin alhakin taimaka wa jam'iyyar wajen gina haɗin kai, gyara ɓarakar da ta taso, da kuma sake tsara jam'iyyar a matsayin fata ta ƙarshe ga al'ummar Jihar Nasarawa gabanin zaɓen shekarar 2027.

Kwamitin Sasanta Rikice-rikicen  wanda zai duba  korafe-korafen da suka shafi zaɓen fidda gwani na gwamna, Sanata da Majalisar Wakilai, zai kasance ƙarƙashin jagorancin tsohon Minista kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa haɗakar ADC a Najeriya, Hon. Barr. Musa Elayo.

Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da:
Hon. Yamusa Chindo
Hon. Sidi Ayigu
Adams Nysana
Audi Sarki Moroa
Aminu Nagogo
Ben Gabi
Hajiya Hauwa Pele
Mrs. Mary Auta
Yayin da Tanimu Zamani zai kasance Sakataren Kwamitin.

A matakin shiyya kuwa, jam'iyyar ta naɗa Hon. Adamu Oyanki a matsayin Shugaban Kwamitin Sasanta Rikice-rikicen zaɓen Majalisar Dokokin Jiha na Nasarawa ta Kudu. 

Mambobin sa sun haɗa da Hon. Obed Mebe, Sadiq Kasimu, Yahaya Oyankpa, yayin da Dr. Taimako Sunday Anyuabaga zai kasance sakatare.
Kwamitin.

 Nasarawa ta Yamma kuwa zai kasance ƙarƙashin jagorancin Ibrahim Baba Mohammed. 

Mambobinsa sun haɗa da Rita Kaya, Ahmed Ohikwo Mohammad, Barr. Kabiru Dogara da Comrade Idris Ojoko a matsayin sakatare.

Jam'iyyar ta kuma amince da naɗin Hon. AbdulKareem Usman a matsayin Shugaban Kwamitin Sasanta Rikice-rikice na Nasarawa ta Arewa.

Sauran mambobin sun haɗa da: Sardauna Kaya
Yusuf Ahmed
Johnson Masin Zhezu
Sai David Attah wanda zai kasance sakatare.

Da ƙaddamar da wannan kwamiti, ADC Nasarawa ta nuna cewa ta zaɓi hanyar haɗin kai maimakon rarrabuwar kawuna. Jam'iyyar ta bayyana cewa tana da ƙudirin kawar da duk wani ɗaci da rashin jituwa tare da fitowa a matsayin madadin da ya dace kuma abin dogaro ga al'ummar jihar.
 

No comments