Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sojoji Sun Ƙaddamar Da Hare-hare Kan Maɓoyar ’Yan Bindiga A Katsina

Rundunar Sojin Nijeriya ta ce ta ƙaddamar da wasu zafafan hare-hare kan ’yan bindiga a wasu yankuna na jihar Katsina da ke arewa maso gabash...




Rundunar Sojin Nijeriya ta ce ta ƙaddamar da wasu zafafan hare-hare kan ’yan bindiga a wasu yankuna na jihar Katsina da ke arewa maso gabashin ƙasar.

Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan mutuwar tsohon Janar na soja a hannun ’yan bindiga.

A wata sanarwa da jami’in yada labarai na rundunar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya fitar ranar Litinin, ya bayyana cewa an fara wannan farmakin mai taken 'Operation Clean Sweep III' domin fatattakar ’yan bindiga a ƙaramar hukumar Matazu da wasu yankunan Katsin.

Ya ce sun fara wannan farmaki ne tun ranar 14 ga watan Yunin 2026.

Rundunar ta ƙaddamar da hare-haren ne ƙarƙashin Operation Fansan Yamma da ke aiki a yankin Arewa maso yammacin ƙasar.

Sanarwar ta ce an samu nasarori musamman a yankunan tsaunukan Dikkawa da sauran ƙauyukan da ke kusa.

Ta ce ta kai samamen ne a yankunan Adua, Nasarawa da Karaduwa, inda ya kai ga gano da lalata maboyar ‘yan ta’adda, wuraren ajiye kayayyaki da sauran cibiyoyin da suke amfani da su.

"A lokacin harin, an lalata maɓoyar ’yan ta'adda da kayayyakinsu da motocinsu, kuma hakan ya rage musu ƙarfin kai hari a yankin," inji sanarwar.

No comments