Mazauna aƙalla ƙauyuka 26 da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sallwato sun fara tara kuɗaɗe domin biyan sabbin harajin da ’yan bindiga...
Mazauna aƙalla ƙauyuka 26 da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sallwato sun fara tara kuɗaɗe domin biyan sabbin harajin da ’yan bindiga suka ƙaƙaba musu, bayan da suka hana manoma zuwa gonakinsu gabanin fara daminar bana.
Majiyoyi daga yankunan da abin ya shafa sun shaida cewa ’yan bindigar sun ba al’ummomin wa’adin kwanaki uku su biya kuɗaɗen da ake nema, tare da gargaɗin cewa babu wanda zai je gona har sai an kammala biyan harajin.
Ƙauyukan da umarnin ya shafa sun haɗa da Garin Faji, Cina Barka, Zululu, Dan Gari, Garin Maigayya, Gardi, Katsira, Garin Baushe, Sulmawa, Zakin Ganga, Dan Kware, Garje, Dogon Faru, Son Allah, Garin Galadima, Kafchi, Matabaya, Garin Labo, Zango, Kaifin Aska, Tsauna Dogo, Tudun Wada, Rambadawa, Ga Itace, Nasarawa da Garin Idi.
Wani mazaunin yankin da ke da kusanci da al’ummomin da abin ya shafa ya bayyana cewa ’yan bindigar sun yi barazanar kashe ko sace duk wanda aka samu yana noma cikin wa’adin kwanaki ukun.
“Sun ce babu wanda zai je gona har sai an biya kuɗin. Duk wanda aka kama yana noma za a kashe shi ko kuma a yi garkuwa da shi, kuma ba zai samu ’yanci ba sai ya biya naira dubu 500,” in ji majiyar.
Ya ce da dama daga cikin mazauna yankunan sun riga sun fara tara kuɗaɗen domin kauce wa sabbin hare-hare, domin suna ganin hakan ne kaɗai mafita a halin yanzu.
Wani mazaunin ƙauyen Zululu, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce yana shirin zuwa gona ranar Juma’a ne kafin ya samu labarin dokar haramta noma.
A cewarsa, ’yan bindigar sun sanar da al’ummomin cewa ba za a ci gaba da ayyukan noma ba har sai an biya harajin da suke karɓa duk shekara.
“An gaya mana cewa sun dakatar da noma na tsawon kwanaki uku har sai an biya harajin da suke karɓa kowace shekara. Sun ce maimakon su bari mutane su je gona su kashe wasu su kuma sace wasu, gara a ba su kuɗin,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa ’yan bindigar sun yi zargin cewa jami’an tsaro na ƙwace musu dabbobi, don haka suka dage cewa ba za a yi noma ba sai an biya kuɗaɗen da suka nema.
Mazaunin ya bayyana cewa ana sa ran sarakunan gargajiya da malaman addini daga ƙauyukan da abin ya shafa za su gana da ’yan bindigar domin sasanta adadin kuɗin da kowace al’umma za ta bayar kafin a ba da damar komawa gonaki.
Ya koka da cewa al’ummomin yankin sun shafe shekaru suna fuskantar irin waɗannan buƙatu, yana mai cewa harajin ya zama wani nauyi mai maimaituwa a kan manoma.
“Muna biyan kuɗi kafin shuka, sannan wani lokaci bayan wata biyu ko uku su sake dawowa su ce ba za a girbi gero ba sai an sake biyan wani harajin,” in ji shi.
A cewarsa, yawanci ’yan bindigar na karɓar tsakanin naira miliyan huɗu zuwa miliyan shida daga kowace al’umma. Daga nan sai a raba wa mazauna kuɗin gwargwadon hali, inda wasu gidaje ke biyan tsakanin naira 1,500 zuwa 2,000, yayin da a wasu ƙauyukan manoma ke biyan har naira 5,000.
Wata majiyar daga Garin Idi, wadda ke zaune a garin Sabon Birni, ta tabbatar da cewa ana ci gaba da tara kuɗaɗe a ƙauyukan da abin ya shafa.
Ya ce ya kai ziyara Garin Idi ranar Juma’a domin jajanta wa al’ummar yankin bayan da aka yi garkuwa da kusan mutum 20 daga ƙauyen da sanyin safiyar ranar.
A cewarsa, ’yan bindigar sun yi zargin cewa an yi jinkiri wajen biyan kuɗaɗen da suka nema, lamarin da ya sa suka kai harin.
“Daga baya sun sanar da shugabannin al’umma cewa sai an biya naira dubu 600 kafin a saki mutanen. An tara kuɗin kuma aka biya, sannan aka sako su ranar Juma’a,” in ji shi.
Da aka tuntuɓi Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufai, ya ce rundunar ba ta samu rahoton irin wannan lamari ba.
“Ba mu da masaniya kan wannan batu. Sau da yawa al’ummomi ba sa kai irin waɗannan rahotanni ga hukumomin tsaro,” in ji shi.
Ƙoƙarin jin ta bakin Gwamnatin Jihar Sokoto bai yi nasara ba. Saƙonnin tes da na WhatsApp da aka aika wa Kakakin Gwamnan Jihar, Abubakar Bawa, da kuma Mai Bai Wa Gwamna Shawara Kan Harkokin Tsaro, Kanal Ahmad Usman (mai ritaya), ba su samu amsa ba har zuwa lokacin kammala wannan rahoto.
.jpg)
No comments