Daga Zubairu Lawal, Lafia Shugaban Tsangayar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Tarayya da ke Lafia ta jihar Nasarawa, Dr. Ikrama Hasan, ya bayyana...
Shugaban Tsangayar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Tarayya da ke Lafia ta jihar Nasarawa, Dr. Ikrama Hasan, ya bayyana cewa shekaru da dama da Mai Martaba Sarkin Lafia, Dr. Sidi Bage Muhammad I, ya shafe yana aikin alƙalanci sun taimaka matuƙa wajen bunƙasa adalci da ci gaban Najeriya.
Dr. Ikrama Hasan ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a wani bangare na bukukuwan murnar cikar Mai Martaba Sarkin Lafia shekaru 70 da haihuwa.
Ya ce tarihin rayuwar Sarkin Lafia ya nuna jajircewa, gaskiya da kishin ƙasa tun daga lokacin da yake aiki a fannin shari’a har zuwa lokacin da ya zama sarki, inda ya ci gaba da bayar da gudunmawa wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin al’umma.
A cewarsa, taron manyan baƙi daga sassa daban-daban na ƙasar nan da suka halarci bikin wata alama ce ta irin mutunci, kima da girmamawar da Sarkin Lafia ke da ita a idon al’umma.
“Idan ka dubi yawan jama’ar da suka hallara a wannan biki, za ka ga sarakunan gargajiya, ‘yan siyasa, manyan jami’an gwamnatin tarayya da na jihar, da sauran fitattun mutane daga sassa daban-daban na ƙasar nan. Wannan ya nuna irin matsayin da Mai Martaba ke da shi a zukatan jama’a,” in ji shi.
Dr. Ikrama ya ƙara da cewa yadda Sarkin Lafia ya tafiyar da rayuwarsa tun yana ma’aikacin shari’a har zuwa matsayinsa na shugaban gargajiya abin koyi ne ga matasa da sauran al’umma.
Ya bayyana cewa Sarkin ya kasance mutum mai kishin adalci, zaman lafiya da ci gaban al’umma, wanda hakan ya sa ya samu karɓuwa a tsakanin mutane ba tare da la’akari da bambancin kabila, addini ko ra’ayin siyasa ba.
Shugaban tsangayar ya yi addu’ar Allah Ya ƙara wa Mai Martaba lafiya, hikima da tsawon rai domin ya ci gaba da ba da gudunmawa ga ci gaban Masarautar Lafia, Jihar Nasarawa da Najeriya baki ɗaya.

No comments