Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

SAƘON SALLAH: Mu Ci Gaba Da Yin Addu'ar Zaman Lafiya, Kwanciyar Hankali, Da Ci Gaban Ƙasa -Minista Idris

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga 'yan Nijeriya da su ci gaba da yi wa ƙasar nan addu’ar samun...


Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga 'yan Nijeriya da su ci gaba da yi wa ƙasar nan addu’ar samun zaman lafiya, kwanciyar hankali, da cigaba a daidai wannan lokaci da suke shagulgulan Babbar Sallah. 

Ministan ya yi kiran ne a ranar wannan Larabar cikin saƙon sa na taya 'yan Nijeriya murnar shagulgulan Sallah. 

Idris ya ce: "A madadin Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta Tarayya, ina miƙa gaisuwar taya murna ga dukkan al’ummar Musulmi a Nijeriya da ma faɗin duniya baki ɗaya a wannan lokaci na Eid al-Adha.

"Wannan biki mai alfarma yana tunatar da mu kyawawan darussa marasa gushewa na imani, sadaukarwa, biyayya, tausayi, da miƙa wuya ga nufin Allah Maɗaukakin Sarki, kamar yadda Annabi Ibrahim (AS) ya nuna.

"Wannan lokaci ne da ke kira a gare mu da mu yi tunani, mu ƙarfafa haɗin kai, haƙuri da juna, da sabunta ƙudirin mu na rungumar kyawawan ɗabi’u da ke haɗa mu a matsayin ƙasa ɗaya.

"Yayin da ’yan Nijeriya suke bikin tare da iyalan su da masoyan su, ina kira ga jama'a da su ci gaba da yi wa ƙasar mu addu’ar samun zaman lafiya, kwanciyar hankali, da cigaba."

Ya ƙara da cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu tana ci gaba da jajircewa wajen aiwatar da manufofin Ƙudirin Sabuwar Fata (Renewed Hope Agenda) tare da gina Nijeriya mafi tsaro da wadata, wadda ta rungumi kowa.

Haka kuma, ya shawarci jama'a da su yi amfani da wannan lokaci wajen nuna ƙauna da tallafi ga marasa galihu, inganta zaman lafiya da zaman tare cikin fahimtar juna, da ƙarfafa ruhin haɗin kan ƙasa ba tare da la’akari da bambancin ƙabila, addini, ko ra’ayin siyasa ba.

Ya kuma yi addu'a da cewa: "Allah Ya sa albarkar wannan bikin Sallah ta kawo zaman lafiya, farin ciki, da yalwar arziki ga kowane gida, kuma Allah Ya karɓi addu’o’in mu da hadayar mu. Barka da Sallah."
 

No comments