Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen ƙaddamar da kashi na farko (Phase 1) na aikin...
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen ƙaddamar da kashi na farko (Phase 1) na aikin titin Kuje zuwa Gwagwalada mai layi biyu a Babban Birnin Tarayya Abuja.Da yake jawabi a wajen taron, Shettima ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Tinubu na ci gaba da shimfiɗa tubalin ci gaba da bunƙasar tattalin arziƙin Najeriya ta hanyar aiwatar da muhimman ayyukan more rayuwa a Abuja da sauran sassan ƙasar nan.
Ya jaddada cewa gwamnatin tarayya ta kuduri aniyar tabbatar da cewa babu wata al’umma da za a bari a baya wajen rabon ayyukan ci gaba, inda ya ce gwamnatin Tinubu na aiki tukuru domin gina Najeriya mai ci gaba, wadata da kyakkyawar makoma ga kowa da kowa.
A cewarsa, ayyukan tituna da sauran manyan ayyukan more rayuwa na daga cikin matakan da gwamnati ke ɗauka domin inganta rayuwar al’umma da bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa.





No comments