Daga Zubairu Lawal, Lafiya Tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa, Kuma Babban Akawun kuɗi, ya bayyana rayuwar Mai Martaba Sarkin ...
Tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa, Kuma Babban Akawun kuɗi, ya bayyana rayuwar Mai Martaba Sarkin Lafia a matsayin abin koyi ga al’ummar Jihar Nasarawa da ma Nijeriya baki ɗaya, sakamakon yadda ya tafiyar da rayuwar sa ta aikin alƙalanci da kuma mulkin sarautar gargajiya cikin adalci, gaskiya da riƙon amana.
Wannan na ƙunshe ne cikin bayanin da Tsohon Kakakin Majalisa Dokokin ya yi, inda ya ce Sarkin Lafia ya kasance jagora mai kishin zaman lafiya da haɗin kai, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban al’umma.
A cewar sa, tun daga lokacin da yake aikin alkalanci har zuwa hawansa karagar mulkin gargajiya, Sarkin Lafia ya kasance mutum mai tsayawa kan gaskiya da adalci ba tare da nuna bambanci ba.
Barade ya ce Sarkin ya taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa haɗin kai tsakanin kabilu daban-daban da mabambantan addinai da ke zaune a faɗin Jihar Nasarawa, lamarin da ya taimaka wajen samar da zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin al’umma.
Ya ƙara da cewa Sarkin Lafia mutum ne mai ƙaunar kowa ba tare da la’akari da ƙabila ko addini ba, inda ya kasance uba ga kowa kuma mai sauraron koke-koke da matsalolin jama’a domin nemo mafita.
“Mai Martaba Sarkin Lafia yana da ƙofar da kowa zai iya zuwa ya gabatar da buƙatarsa. Yana sauraron jama’a cikin haƙuri tare da ba da shawarwari da mafita ga matsalolinsu,” in ji Barade.
Ya bayyana cewa duk lokacin da sarakuna, shugabanni ko talakawa suka fuskanci wata matsala da ta gagare su, sukan nemi taimakon Sarkin Lafia, wanda galibi ke taka rawa wajen sasanta rikice-rikice da warware sabani cikin hikima da adalci.
Ahmad Muhammad Barade ya yabawa irin gudunmawar da Sarkin Lafia ke bayarwa wajen haɗa kan sarakunan gargajiya, shugabannin siyasa da talakawa domin samar da kyakkyawan shugabanci da ci gaban al’umma.
Ya yi addu’ar Allah ya ci gaba da ba Mai Martaba Sarkin Lafia lafiya, hikima da tsawon rai domin ci gaba da yi wa masarautarsa da al’ummar Jihar Nasarawa hidima.

No comments