Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta shirya zaman addu’o’i na musamman domin neman zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban Nijeriya a wani bangar...
Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta shirya zaman addu’o’i na musamman domin neman zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban Nijeriya a wani bangare na ayyukan ranar Arafat a Hajjin shekarar 2026.
An gudanar da addu’o’in ne a ranar Talata a birnin Makkah yayin da miliyoyin alhazai daga sassa daban-daban na duniya suka hallara a Dutsen Arafat domin gudanar da rukuni mai muhimmanci na aikin Hajji.
Zaman addu’ar ya samu halartar mambobin Kwamitin Malamai na Kasa na NAHCON, wasu ‘yan majalisar tarayya, jami’an hukumar da kuma maniyyata daga Nijeriya.
Shugaban Hukumar NAHCON kuma Babban Jami’in gudanarwa, Ambasada Ismail Abba Yusuf, ya bayyana cewa hukumar ta shirya addu’ar ne saboda halin malubalen tattalin arziki da zamantakewar da ƙasar ke ciki.
Ambasada Yusuf wanda Kwamishinan Tsare-tsare, Bincike, Watsa Labarai da Ayyukan Laburare na hukumar, Farfesa Abubakar Yagawal ya wakilta, ya ce irin waɗannan ƙalubale suna buƙatar ‘yan Nijeriya su koma ga Allah domin neman taimako da mafita.
Ya kuma buƙaci maniyyatan Nijeriya da su riƙa sanya ƙasar cikin addu’o’insu yayin da suke roƙon buƙatunsu na ƙashin kai.
Shi ma da yake jawabi, ɗan majalisar wakilai, Hon. Aliyu Sani Madaki, ya yaba wa shugabancin hukumar NAHCON bisa shirya addu’ar, yana mai cewa hakan ya nuna kishin ƙasa da kula da makomar al’umma.
An gudanar da addu’o’in ne cikin harsunan Larabci da Turanci tare da wasu harsunan Nijeriya da suka haɗa da Hausa, Yarbanci, Igbo, Nupe da Afemai.
A wani saƙo na musamman da ya aikewa maniyyatan Najeriya a ranar Arafat, shugaban NAHCON ya bayyana ranar a matsayin rana mafi girma a aikin Hajji, wadda take cike da rahama, gafara da karbar addu’a.
“Arafat rana ce ta tawali’u da sadaukarwa da kuma komawa ga Allah cikin cikakkiyar biyayya. Lokaci ne na yin nazari a kan rayuwa da kuma sabunta alkawarin bautar Allah da hidima ga bil’adama,” in ji shi.
Ya ce hukumar ta NAHCON na ci gaba da nazarin abubuwan da suka shafi ayyukan Hajji domin ƙara inganta jin daɗin maniyyata da saukaka musu gudanar da ibadun su.
“Mun yi nisa daga shekarun baya da alhazai ke ɗaukar lokaci mai tsawo a sansanonin jirgi kafin tashinsu zuwa Saudiyya zuwa yadda ake gudanar da Hajji cikin tsari da sauƙi a yanzu,” in ji Yusuf.
Sai dai ya ce duk da nasarorin da aka samu, har yanzu akwai buƙatar kara gyare-gyare domin inganta ayyukan Hajji a nan gaba.
Shugaban hukumar ya kuma yaba wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa goyon bayan da take bai wa hukumar, wanda ya ce hakan ya taimaka wajen samun nasarorin da aka samu a jigilar maniyyatan bana.
Haka kuma ya gode wa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, bisa bayar da jagoranci da sa ido kan aiwatar da manufofin da suka shafi aikin Hajji.
Ya kuma yabawa jami’an hukumar NAHCON da sauran masu ruwa da tsaki saboda jajircewa da sadaukarwa wajen gudanar da aikin Hajjin bana.
Daga ƙarshe, Yusuf ya tabbatar wa maniyyata cewa hukumar ta dauki matakan da suka dace domin tabbatar da dawowar su gida cikin tsaro da kwanciyar hankali bayan kammala aikin Hajji.
“Allah Ya karbi ibadun mu, Ya gafarta mana kura-kuran mu, Ya haɗa kanmu tare da ba mu zaman lafiya da ci gaba,” in ji shi.

No comments