Daga Zubairu Lawal, Lafia Barrista Isyaka Mudi Dikko (SAN) ya bayyana matuƙar farin cikin sa tare da taya Mai Martaba Sarkin Lafia, Dr. Sidi...
Daga Zubairu Lawal, Lafia
Barrista Isyaka Mudi Dikko (SAN) ya bayyana matuƙar farin cikin sa tare da taya Mai Martaba Sarkin Lafia, Dr. Sidi Bage Muhammad I murnar cika shekaru 70 da haihuwa.
Da yake zantawa da manema Labarai, Barrista Dikko ya yaba da irin gudumawa da alherin da Sarkin Lafia ya bayar wajen bunƙasa zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban al’umma a Jihar Nasarawa.
Ya bayyana cewa Dr. Sidi Bage, wanda tsohon Alƙalin Kotun Ƙoli ne, ya yi fice wajen amfani da hikima da kwarewarsa wajen jagoranci, lamarin da ya taimaka wajen ƙarfafa zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al’ummomin jihar.
Barrista Dikko ya ƙara da cewa a ƙarƙashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Lafia, an samu kyakkyawar alaƙa da haɗin kai tsakanin kabilu daban-daban da ke zaune a Jihar Nasarawa, wanda hakan ya taimaka wajen inganta zaman tare cikin lumana da mutunta juna.
Ya ce ayyukan alherin da Sarkin Lafia ke yi, da kuma kokarinsa na tabbatar da zaman lafiya da ci gaban masarautarsa da jihar baki ɗaya, sun sa ya zama abin koyi ga sauran shugabannin gargajiya a ƙasar nan.
Barrista Isyaka Mudi Dikko SAN ya yi addu’ar Allah Ya ƙara wa Mai Martaba lafiya, tsawon rai, hikima da ƙarfi domin ci gaba da yi wa al’umma hidima.

No comments