Daga Zubairu Lawal,Lafia Ɗan takarar gwamna na Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaɓen shekarar 2027, Sanata Ahmed Aliyu Wadada, ...
Daga Zubairu Lawal,Lafia
Ɗan takarar gwamna na Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaɓen shekarar 2027, Sanata Ahmed Aliyu Wadada, ya amince da tikitin takarar da jam’iyyarsa ta ba shi, tare da alƙawarin ci gaba da gina kan nasarorin da gwamnatin yanzu ta samu da kuma jagorantar jihar ta hanyar gwamnati mai mayar da hankali ga buƙatun al’umma.
Da yake jawabi a wani taron manema labarai da aka gudanar a Lafia, Sanata Wadada ya bayyana fitowarsa a matsayin ɗan takarar APC a matsayin nasara ga dimokuraɗiyya, haɗin kai, ci gaba da kuma muradun al’ummar Jihar Nasarawa.
Ya nuna godiyarsa ga mambobin APC a faɗin jihar bisa irin amincewa da suka nuna masa, tare da tabbatar musu da jajircewarsa wajen samar da shugabanci mai gaskiya, haɗin kai da kuma mayar da hankali wajen cimma sakamako.
Dan takarar APC ɗin ya yaba wa shugabannin jam’iyyar bisa yadda suka gudanar da zaɓen fidda gwani na gwamna cikin lumana, gaskiya, sahihanci da nasara.
Musamman, ya yabawa Shugaban APC na Jihar Nasarawa, Dakta Aliyu Bello, mambobin Kwamitin Gudanarwa na Jiha da jami’an zaɓe bisa tabbatar da gudanar da sahihin zaɓe cikin adalci da gaskiya.
Sanata Wadada ya yi wa Gwamna Abdullahi Sule yabo mai yawa, inda ya bayyana shugabancinsa a matsayin mai manufa, balaga da hangen nesa.
A cewarsa, Gwamna Sule ya shimfiɗa tubali mai ƙarfi na ci gaba mai ɗorewa ta hanyar nasarorin da ya samu a fannoni daban-daban kamar ababen more rayuwa, masana’antu, noma, lafiya, ilimi, tsaro da sauya fasalin tattalin arziki.
Ya kuma gode wa gwamnan bisa goyon baya da jajircewarsa wajen tabbatar da ci gaban Jihar Nasarawa.
Hakazalika, ɗan takarar gwamnan na APC ya yabawa sauran masu neman takarar gwamnan, ciki har da Hassan Liman da Dakta Fatima Abdullahi, bisa yadda suka nuna dattako wajen amincewa da sakamakon zaɓen fidda gwani.
Ya yi kira ga dukkan masu neman takara, magoya bayansu da masu ruwa da tsaki a jam’iyyar da su haɗa kai domin tabbatar da nasarar APC a babban zaɓen shekarar 2027.
“Babu mai nasara, babu kuma wanda aka kayar. Dukkanmu ’ya’yan gida ɗaya ne na siyasa, muna da buri guda na zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban Jihar Nasarawa,” in ji shi.
Manhajar HEARTS Domin Ci Gaba
Yayin da yake bayyana tsarin ci gaban gwamnatinsa mai taken HEARTS Agenda.
Wadada ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hankali kan:
H – Human Capital Development (Bunkasa Jarin Dan Adam)
E – Economic Enhancement (Inganta Tattalin Arziki)
A – Accountability (Rikon Amana da Gaskiya)
R – Rural Transformation (Ci gaban Karkara)
T – Technological Advancement (Ci gaban Fasaha)
S – Security (Tsaro)
Ya bayyana cewa an tsara wannan manhaja ne domin ƙarfafa nasarorin da aka samu tare da samar da sabbin damammaki na bunƙasa tattalin arziki, ƙarfafa matasa, raya karkara, ƙirƙire-ƙirƙire da inganta tsaro.
Dan takarar APC ya yi alƙawarin kafa gwamnati mai gaskiya, rikon amana da haɗa kowa da kowa, wadda za ta fifita jin daɗin al’umma, ƙarfafa cibiyoyi, faɗaɗa damar tattalin arziki da kuma jawo masu zuba jari.
Sanata Ahmad Wadada, ya kuma bayyana goyon bayansa ga manufar Renewed Hope Agenda ta Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa na da nufin samar da dawwamammen ci gaba, kwanciyar hankali da wadata ga ƙasa.
Ya yaba da jagorancin Shugaba Tinubu tare da jaddada aniyarsa ta goyon bayan ƙoƙarin gwamnatin tarayya wajen sauya tattalin arziki, inganta tsaro da ƙarfafa dimokuraɗiyya.
A ƙarshe, Sanata Wadada ya gode wa sarakunan gargajiya, mata, matasa, masu buƙata ta musamman, shugabannin addinai, masu ruwa da tsaki al’umma da kuma mambobin APC a dukkan mazabu 147 na jihar bisa goyon bayan da suka ba shi.
Ya yi kira ga al’ummar jihar da su kauce wa bambance-bambancen siyasa tare da rungumar haɗin kai, yana mai bayyana yakinin cewa mafi kyawun kwanaki ga Jihar Nasarawa suna gaba.
“Tare za mu iya gina Jihar Nasarawa mai samar da ƙarin damammaki ga matasanmu, ingantaccen kiwon lafiya ga iyalanmu, ilimi mai nagarta ga yaranmu, tsaro mai ƙarfi ga al’ummominmu da kuma wadata mai ɗorewa ga kowa da kowa,” in ji shi.

No comments