Mataimakin Shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya bayyana cewa shirye-shirye da manufofin Shugaba Bola Ahmed Tinubu an shirya suna ta yad...
Mataimakin Shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya bayyana cewa shirye-shirye da manufofin Shugaba Bola Ahmed Tinubu an shirya suna ta yadda za su mori matasan Nijeriya, saboda gwwmnati na amfani da sabbin dabaru wajen magance matsalolin zamani na wannan karni na 21.
Ya yi wannan bayani ne yayin ganawa da shugabannin ƙungiyar City Boy Movement a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda ya jaddada cewa gwamnati na ɗaukar matasa a matsayin ginshiƙin ci gaban ƙasa da kuma makomar dimokuraɗiyya.
Shettima ya ce gwamnatin Tinubu na ɗaukar matakai masu wahala amma masu muhimmanci don farfaɗo da tattalin arziki da kuma tabbatar da ci gaba mai dorewa, yana mai cewa nasarar gyare-gyare na buƙatar haƙuri, jajircewa da goyon bayan ‘yan ƙasa.
Ya kuma bayyana cewa dimokuraɗiyya ba ta tsaya kan zabe kaɗai ba, tana buƙatar shigar jama’a da kuma haɗin kai wajen kare manufofin da ke kawo ci gaba ga ƙasa.
Mataimakin Shugaban Ƙasa ya yabawa ƙungiyar City Boy Movement bisa ƙokƙarinta na wayar da kan jama’a da kuma ƙarfafa goyon bayan gwamnati, yana mai jaddada muhimmancin ladabi, amana da hadin kai a siyasa da shugabanci.
Ƙungiyar wadda Hon. Francis Oluwatosin Shoga, ke jagaranta ta yi alƙawarin ci gaba da zagayawa fadin Najeriya domin tattara goyon baya ga sake zaben Shugaba Tinubu a shekarar 2027.











No comments