Gwamnatin Ƙasar Birtaniya ta sake nuna amincewarta da salon mulkin Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, inda ta yaba da sauye-sauyen da gw...
Yabon ya fito ne daga Ministar Harkokin Raya Ƙasa da Afirka ta Birtaniya, Jenny Chapman, yayin wata ziyarar aiki da ta kai gidan gwamnatin jihar Kaduna domin duba tasirin ayyukan haɗin gwiwa da Birtaniya ke tallafawa a fannoni daban-daban.
Ministar ta bayyana cewa gwamnatin Uba Sani ta nuna jajircewa wajen aiwatar da gyare-gyaren da suka ƙarfafa cibiyoyin gwamnati, inganta gaskiya da riƙon amana tare da samar da shugabanci mai hangen nesa da ke amfani ga al’umma.
Ta kuma yaba da gagarumin ci gaban da jihar ta samu a fannin zaman lafiya da tsaro, tana mai cewa wannan nasara ce da ta samar da yanayi mai kyau ga bunƙasar tattalin arziki da jawo masu zuba jari.
Jenny Chapman ta tabbatar da cewa gwamnatin Birtaniya za ta ci gaba da tallafa wa Kaduna a fannoni kamar ilimi, lafiya, kariyar jin daɗin al’umma, muhalli da noma domin taimaka wa jihar wajen cimma manufofin ci gabanta.
Da yake mayar da martani, Gwamna Uba Sani ya bayyana haɗin gwiwar Kaduna da Birtaniya a matsayin mai amfani da kuma mai haifar da sakamako mai kyau ga al’ummar jihar.
Ya ce shirye-shiryen haɗin gwiwa irin su SLGP, SPARC, SAVI, PERL da PACE sun taka muhimmiyar rawa wajen mayar da Kaduna ɗaya daga cikin jihohin da suka yi fice a fannin gyaran tsarin mulki da gudanar da gwamnati a Najeriya.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa Kaduna na daga cikin jihohin farko a Afirka da suka rungumi tsarin Open Government Partnership (OGP), wanda ke ƙarfafa gaskiya, shiga tsakanin gwamnati da al’umma da kuma riƙon amana.
Haka kuma, ya bayyana cewa jihar ta samu fiye da kashi 500 cikin 100 na ƙaruwa a kuɗaɗen shiga na cikin gida (IGR), sakamakon gyare-gyaren da aka aiwatar wajen tara kuɗaɗen shiga da inganta ayyukan hukumomin gwamnati.

No comments