Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

’Yan Ta’adda Sun Halaka 'Yan Sanda 17 Suna Tsaka Da Ɗaukar Horo A Yobe

Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta tabbatar da mutuwar jami’anta 17 bayan wani mummunan harin ’yan ta’adda da aka kai makarantar horas da rund...


Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta tabbatar da mutuwar jami’anta 17 bayan wani mummunan harin ’yan ta’adda da aka kai makarantar horas da rundunar musamman ta Sojojin Nijeriya da ke Buni Yadi, ƙaramar hukumar Gujba a jihar Yobe.

Rahotanni sun bayyana cewa harin ya faru ne da sanyin safiyar ranar 8 ga watan Mayu a cibiyar horaswar sojin, inda jami’an ’yan sandan ke karɓar horo na musamman kan dabarun yaƙi da ta’addanci da gudanar da ayyukan tsaro.

A wata sanarwa da Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya, ACP Anthony Okon Placide, ya aikewa manema labarai a ranar Asabar, rundunar ta ce ’yan ta’addan sun kai farmaki makarantar ne daga wurare daban-daban da misalin ƙarfe 1:15 na dare.

Sanarwar ta bayyana cewa jami’an da suka mutu sun rasa rayukansu ne yayin da suke cikin horon ƙwarewa na ayyukan musamman a makarantar.

“Jami’an da ke karɓar horo na musamman a cibiyar sun rasa rayukansu bayan ’yan ta’adda sun kai hari daga sassa daban-daban na makarantar da misalin ƙarfe 1:15 na dare,” in ji sanarwar.

Rundunar ta kuma bayyana cewa wasu jami’an Sojojin Nujeriya sun mutu yayin da suke ƙoƙarin daƙile harin a fafatawar bindiga mai zafi da aka yi tsakanin sojoji da maharan.

Da yake martani kan lamarin, Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya bayyana jami’an da suka mutu a matsayin jarumai masu kishin ƙasa da suka sadaukar da rayuwarsu wajen kare Nijeriya.

Sanarwar ta ambato Sufeto Janar ɗin yana cewa jami’an sun nuna “gagarumar kishin ƙasa da jajircewa wajen kare tsaron ƙasa” ta hanyar shiga horon yaƙi da ta’addanci da dabarun tsaro na zamani.

Ya kuma miƙa ta’aziyyar Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ga iyalan mamatan, tare da tabbatar musu cewa ba za a taɓa mantawa da sadaukarwar ’ya’yansu ba.

A wani yunƙuri na nuna alhini da ƙarfafa guiwar jami’an da suka tsira, Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar Yobe, Usman Kanfani Jibrin, ya kai ziyara makarantar horaswar a madadin Sufeto Janar na ’Yan Sanda.

Yayin ziyarar, ya jajanta wa kwamandan makarantar, A.C. Enuagu, da jami’an Sojojin Nijeriya tare da sauran jami’an ’yan sanda da suka tsira daga harin.

Hakazalika, ya yabawa juriyar jami’an da suka tsira, inda ya buƙace su da su ci gaba da kammala horon domin girmama abokan aikinsu da suka rasa rayukansu.

Rundunar ’yan sandan ta kuma tabbatar wa ’yan Najeriya cewa hukumomin tsaro sun ƙara kaimi wajen farautar waɗanda suka kai harin domin gurfanar da su a gaban doka.

“Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya na girmama jarumta, sadaukarwa da hidimar jami’an da suka mutu, waɗanda ƙasa za ta ci gaba da tunawa da su har abada,” in ji sanarwar.

No comments