Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

’Yan Sanda Sun Gurfanar Da Baffa Hotoro A Kotu Kan Batanci Ga Sheikh Dahiru Bauchi

Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta shigar da ƙara a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan  wani malami a jihar Kano, Adam Zubair Adam, wa...




Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta shigar da ƙara a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan  wani malami a jihar Kano, Adam Zubair Adam, wanda aka fi sani da Baffa Hotoro, bisa zargin yin batanci ta kafafen sadarwar zamani, barazana da kuma wasu laifuka da suka shafi manyan malamai irin su Sheikh Dahiru Usman Bauchi da Sheikh Mannir Adam Koza.

Takardun ƙarar mai ƙunshe da tuhume-tuhume guda shida sun fito ne daga Sashen Shari’a na Hedikwatar Rundunar ’Yan Sandan Najeriya da ke Abuja, inda lauyoyin gwamnati M.K. Yahaya da R.N. Maigoro da kuma A.I. Aminu suka sanya hannu a kai.

A cewar bayanan kotu, an gurfanar da Sheikh Baffa Hotoro ne bisa tanade-tanaden sashe na 24(1)(b) na Dokar Yaki da Laifukan Yanar Gizo ta shekarar 2015 da aka yi wa kwaskwarima a 2024.

Takardun shari’ar mai lamba FHC/ABJ/CR/87/2026 sun nuna cewa Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya ne mai ƙara, yayin da Sheikh Baffa Hotoro yake matsayin wanda ake ƙara.

Bayanan kotun sun bayyana cewa an shirya gurfanar da malamin a ranar Litinin 11 ga watan Mayun 2026 a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, amma hakan bai samu ba bayan ya kasa halartar zaman kotun.

Rahotanni sun nuna cewa an isar masa da sammaci da sauran takardun kotu yadda ya kamata, sai dai bai bayyana a kotun ba, kuma bai bayar da wani bayani kan rashin zuwansa ba.

Marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu a ranar 25 ga watan Nuwamban 2025, na daga cikin manyan malaman Musulunci masu tasiri a Najeriya da yankin Afirka ta Yamma, kuma jagora ne a ɗarikar Tijjaniyya da ke da miliyoyin mabiya.

Shi ma Sheikh Mannir Adam Koza ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin matasan malaman Tijjaniyya masu tasiri a Najeriya.

A gefe guda kuma, Sheikh Baffa Hotoro sanannen malamin Salafiyya ne da hudubobinsa suka sha haifar da ce-ce-ku-ce, musamman wajen suka ga malamai da jagororin ɗarikar Sufaye.

Takardun kotun sun bayyana cewa a ranar 18 ga watan Yunin 2024, Baffa Hotoro ya yi wasu kalamai da ake zargin na cin mutunci ne ga malaman biyu, inda ya rantse da Allah cewa su mushrikai ne kuma Allah bai amince su shiga Ka’aba ba.

A cikin wani bidiyo na Hausa da ya bazu a kafafen sada zumunta, an ce malamin ya bayyana cewa:

> “Na rantse da Allah, Munir Koza yana cikin waɗanda Allah bai yarda su ziyarci Ɗakinsa Mai Alfarma ba. Dahiru Usman Bauchi shugaban sharri ne, kuma yana cikin waɗanda Allah bai yarda su shiga Harami ba. Waɗannan mushrikai ne...”

Rundunar ’yan sandan ta kuma bayyana cewa a ranar 19 ga watan Mayun 2023, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta kama Baffa Hotoro bayan koke-koken jama’a da gwamnatin jihar Kano kan kalamansa da suka shafi Sheikh Dahiru Bauchi.

Daga baya an ga wani bidiyo inda ya nemi afuwa ga marigayin malamin da iyalansa da mabiyansa.

Sai dai bayan rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi a watan Nuwamban 2025, an ce Hotoro ya sake fitar da wani bidiyo mai ɗauke da sababbin kalamai masu tayar da hankali, waɗanda aka bayyana cewa za su iya haddasa rikicin addini da barazana ga tsaron ƙasa.

Bayan koken da iyalan marigayin da Sheikh Mannir Koza suka kai wa hukumomi, an sake kama Hotoro a watan Fabrairu na wannan shekara kafin daga bisani a bayar da belinsa.

A cikin tuhume-tuhumen, ’yan sanda sun zarge shi da wallafa bidiyoyin ƙarya a shafukansa na TikTok da Facebook domin haifar da tsana da razana Sheikh Mannir Koza da marigayi Sheikh Dahiru Bauchi.

Sauran tuhume-tuhumen sun haɗa da kiransu “mushrikai”, da kuma furta kalaman da za su iya tayar da husuma tsakanin mabiyan Tijjaniyya.

Takardun ƙarar sun bayyana cewa lauyan Compass Chambers, Barista M.M. Nasir, ne ya gabatar da koken a madadin Sheikh Mannir Koza da iyalan marigayi Sheikh Dahiru Bauchi zuwa ofishin Sufeto Janar na ’Yan Sanda.

Masu ƙarar sun yi zargin cewa kalaman Hotoro na iya tayar da tarzoma da fusata miliyoyin almajirai da mabiyan marigayin malamin.

Wasu malamai daga bangarorin Sufaye da Salafiyya a jihohin Kano da Kaduna da Jigawa da Katsina da Bauchi da Gombe da Jos sun bayyana matakin shari’ar a matsayin wani babban mataki na tsaftace tsarin wa’azi a Arewacin Nijeriya.

Wani malami mai suna Ustaz Muhammad Sagir ya ce shari’ar na iya rage rikicin mazhabobi da hana yawaitar furucin da ke haddasa fitina tsakanin malamai.

Shi ma Malam Yusuf al-Maliky ya bayyana cewa matakin zai taimaka wajen ƙarfafa fahimtar juna tsakanin mazhabobi tare da dakile kalaman da ba su dace daga masu wa’azi.

Lauyoyi ma sun yaba da yadda masu ƙarar suka bi hanyar doka maimakon ɗaukar doka a hannunsu, suna mai cewa addini batu ne mai matuƙar muhimmanci da sarkakiya a Arewacin Najeriya.

Ƙoƙarin jin ta bakin Sheikh Baffa Hotoro bai yi nasara ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, domin bai amsa saƙonnin tes ko na WhatsApp da aka tura masa ba.

No comments