Daga cikin matakan da hukumomin tsaro ke ɗauka na daƙile ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas, dakarun sojin Nijeriya tare da haɗin ...
Rahotanni sun ce an gudanar da harin ne a daren jiya bayan samun bayanan sirri da suka nuna inda jagoran kungiyar da wasu manyan kwamandojinsa suke boye.
Majiyoyi sun bayyana cewa samamen ya kuma yi sanadin kashe wasu daga cikin na hannun damansa tare da lalata sansanonin da ake zargin kungiyar na amfani da su wajen tsara hare-hare a yankin Tafkin Chadi da wasu sassan Arewa maso Gabas.
An ce aikin haɗin gwiwar ya gudana cikin kwarewa, inda aka yi amfani da bayanan leƙen asiri da kuma kayan aiki na zamani wajen kai harin ba tare da bata lokaci ba.
Da yake mayar da martani kan nasarar aikin, Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yaba wa haɗin gwiwar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka, yana mai cewa hakan na nuna muhimmancin zumuncin ƙasashen biyu wajen yaƙi da ta’addanci.
“Ina miƙa godiyata ta musamman ga Shugaba Donald Trump saboda jagorancin sa da kuma goyon bayan da Amurka ke bai wa Nijeriya a wannan fafutuka,” in ji shugaban.
Tinubu ya kuma jinjinawa dakarun da suka gudanar da aikin daga bangarorin biyu saboda bajinta da ƙwarewar da suka nuna wajen aiwatar da samamen.
“Munanan hare-hare irin wannan su ci gaba da fadawa maboyar ‘yan ta’adda a duk inda suke a faɗin ƙasar nan,” in ji shi.
Masana harkokin tsaro na ganin hallaka Abu-Bilal Al-Manuki na iya zama babbar koma baya ga ayyukan ƙungiyar IS a yankin Tafkin Chadi, musamman ganin yadda ake alakanta shi da shirya hare-hare da safarar makamai a tsakanin ƙasashen yankin.
A ‘yan shekarun baya-bayan nan, Nijeriya ta ƙara karfafa haɗin gwiwar tsaro da ƙasashen duniya domin daƙile matsalar ta’addanci da ta addabi wasu sassan kasar, musamman Arewa maso Gabas.

No comments