Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya isa Legas a ranar Juma’a bayan ziyarar da ya kai ƙasashe uku—Faransa, Kenya da Ruwanda. Mai Bai wa Shugaban Ƙas...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya isa Legas a ranar Juma’a bayan ziyarar da ya kai ƙasashe uku—Faransa, Kenya da Ruwanda.
Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya faɗa a wata sanarwar manema labarai da ya sanya wa hannu cewa jirgin Tinubu ya sauka da misalin ƙarfe 7:12 na yamma a ɓangaren shugaban ƙasa na Babban Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja.
Waɗanda suka tarbe shi sun haɗa da Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu; Mataimakin Gwamna, Femi Hamzat; Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila; Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Legas, Mudashiru Obasa, da sauran jami’an gwamnati.
Yayin da yake Faransa, Shugaba Tinubu ya gana da masu zuba jari na duniya, inda ya jaddada gaskiya da bin ƙa’idojin kuɗi, tare da bayyana dalilan gaggauta aiwatar da manyan sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin sa ta ƙaddamar.
Ya kuma halarci taron "Africa Forward Summit" a Nairobi, Kenya, wanda Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Shugaban Kenya William Ruto suka jagoranta tare.
A wurin taron, Tinubu ya yi kira da a sake fasalin tsarin kuɗaɗen duniya tare da ƙarfafa haɗin gwiwar tattalin arziki da zai fifita cigaban Afrika da wadata.
Ya bayyana irin damar da Nijeriya take da ita a fannin tattalin arzikin teku a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan cigaban Afrika, tare da alƙawarin raba tsarin bayanan leƙen asirin harkokin teku na Nijeriya da ƙasashen yankin Tekun Guinea da suke da sha’awar hakan.
A Nairobi, Shugaban ya kuma gana da takwaran sa na Madagaska, Michael Randrianirina, a wata ganawar ƙasashe biyu.
A Kigali, babban birnin ƙasar Ruwanda, Shugaba Tinubu ya haɗu da sauran shugabannin Afrika, da masu zuba jari, da manyan shugabannin kamfanonin duniya da na Afrika a taron "Africa CEO Forum", domin tattauna hanyoyin gaggauta sauyin tattalin arzikin nahiyar ta hanyar faɗaɗa haɗin gwiwa, haɗewar yankuna, da ƙara zuba jari tsakanin ƙasashe.
Ya kuma gana da shugaban Ruwanda kuma mai masaukin baƙi, Paul Kagame.
Haka kuma ya gana da wakilan kamfanoni da cibiyoyi na ƙasa da ƙasa, ciki har da International Finance Corporation (IFC), APM Terminals, da Winme Group, inda aka samu sakamako masu kyau.
Tinubu ya kuma shiga tattaunawa da zaman kwamitoci da suka bayyana manufofin shirye-shiryen sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin sa.
A lokacin da yake Legas, Shugaban Ƙasa zai halarci zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC da za a fara ranar Asabar.
Tun da farko, a cikin wata sanarwa da ya aike wa membobin jam’iyyar, Tinubu ya buƙaci duk masu halartar zaɓen fidda gwanin da su “kiyaye zaman lafiya kuma su kasance masu nuna wasa da tsare gaskiya da adalci domin moriyar jam’iyya da ƙasar mu baki ɗaya.”

No comments