Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Tinubu Ya Gana Da Manyan Masu Zuba Jari Na Duniya A Birnin Paris

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gana da manyan masu zuba jari na duniya a birnin Paris na ƙasar Faransa, inda ya jaddada aniyar gwamnatin sa na...

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gana da manyan masu zuba jari na duniya a birnin Paris na ƙasar Faransa, inda ya jaddada aniyar gwamnatin sa na tabbatar da gaskiya, adalci, da kuma kiyaye ka’idojin kashe kuɗi. Shugaban ya kuma bayyana dalilan da suka sa aka aiwatar da garambawul ga tattalin arziki cikin gaggawa.

A yayin taron, Ministan Kuɗi da Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele, ya bayyana nasarorin da Najeriya ta samu, inda ya ce tattalin arzikin ƙasar ya haɓaka da kashi 11.2% (idan aka lissafa da dalar Amurka) a shekarar 2025.

A cewarsa, wannan ci gaba ya nuna cewa burin Najeriya na ganin tattalin arzikinta ya kai darajar dala triliyan ɗaya ($1 trillion) nan da shekarar 2030 zai iya tabbata. Oyedele ya kuma lashi takobin cewa gwamnati za ta riƙa wallafa bayanan kuɗi na kowane bayan watanni uku domin tabbatar da gaskiya.

Muhimman Abubuwan Da Aka Tattauna:
• Bashin Ƙasa: Shugabar Ofishin Kula da Basussuka (DMO), Patience Oniha, ta tabbatar wa masu zuba jarin cewa gwamnati tana amfani da bashi ta hanyar da ta dace kuma za ta tabbatar ba a jefa ƙasar cikin halin kaka-ni-kayi ba.
• Tsaro da Man Fetur: Shugaba Tinubu ya bayyana cewa gwamnati na ƙoƙarin gyara harkar mai don daina tafka asara, sannan ana shirin rarraba ikon rundunar 'yan sanda (decentralisation) don magance matsalar tsaro da kuma toshe hanyoyin samar wa 'yan ta'adda kuɗi.
• Makomar 2027: Lokacin da aka tambaye shi game da shirinsa na bayan shekarar 2027, Shugaban ya yi alkawarin ci gaba da ƙarfafa tsarin tattalin arziki da tabbatar da cewa ba a canza manufofin da aka sa gaba ba.

Taron ya samu halartar wakilai daga manyan kamfanoni na duniya, ciki har da:
1.    Citibank da Amundi (Faransa) karkashin jagorancin Valerie Baudson.
2.    BlueCrest da Ninety One (Biritaniya da Afirka ta Kudu).
3.    Kirkoswald Capital, Principal Finisterre, da PGIM (Amurka).

Masu zuba jarin sun yaba da matakan gyara da Shugaba Tinubu ya ɗauka, inda suka nuna kyakkyawan fata kan makomar tattalin arzikin Najeriya.

 

No comments