Daga Zubairu Lawal, Lafia Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Hon. Abubakar Hassan Na-Laraba ya miƙa godiya ta musamman ga ɗimbin magoya bayan Jam’...
Daga Zubairu Lawal, Lafia
Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Hon. Abubakar Hassan Na-Laraba ya miƙa godiya ta musamman ga ɗimbin magoya bayan Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a faɗin Jihar Nasarawa, musamman a Mazabar Sanatan Nasarawa ta Kudu, bisa gagarumin goyon bayan da suka bayar wanda ya kai ga fitowar sa a matsayin ɗan takarar Sanata na APC domin zaɓen shekarar 2027.
A cikin wata sanarwa da Shugaban Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen, Barr. MT Alakayi ya sanya wa hannu, kwamitin ya bayyana cewa soyayya, amincewa da goyon bayan da al’umma suka nuna wa Hon. Na-Laraba abin alfahari ne da ba za a manta da shi ba.
Sanarwar ta jaddada cewa nasarar da aka samu ba ta Hon. Na-Laraba kaɗai ba ce, illa nasara ce ta ɗaukacin al’ummar Mazabar Sanatan Nasarawa ta Kudu da kuma APC baki ɗaya.
Kwamitin ya kuma yi kira ga sauran masu neman takara da magoya bayansu da su rungumi ruhin haɗin kai da siyasa mai tsafta, tare da fifita muradun jam’iyyar sama da duk wata buƙata ta kashin kai domin tabbatar da nasarar APC a babban zaɓen 2027.
“Masu nasara masu ɗaukar tutar jam’iyya ne kawai, amma nasarar APC tana hannun dukkan mambobi da magoya bayan jam’iyyar,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta yabawa dukkan waɗanda suka shiga zaɓen fidda gwani bisa jajircewa da gudunmawar da suka bayar wajen tabbatar da nasarar tsarin dimokuraɗiyya a jam’iyyar.
Kwamitin ya bayyana Hon. Na-Laraba a matsayin shugaba mai dattako, karamci da kishin ci gaban al’umma, yana mai cewa ya yi imani da haɗin kai da zaman lafiya a matsayin ginshiƙan ci gaba mai ɗorewa.
A ƙarshe, kwamitin ya yi addu’ar Allah Ya albarkaci APC, Mazabar Sanatan Nasarawa ta Kudu, Jihar Nasarawa da kuma Tarayyar Najeriya baki ɗaya.

No comments