Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

2027: Ombugadu Zai Yi Wa PDP Ta Karar Gwamnan Jihar Nasarawa

Daga Zubairu Lawal, Lafia Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Jihar Nasarawa ta tabbatar da Dr. Emmanuel David Ombugadu a matsayin ɗa...


Daga Zubairu Lawal, Lafia

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Jihar Nasarawa ta tabbatar da Dr. Emmanuel David Ombugadu a matsayin ɗan takararta na gwamna domin zaɓen shekarar 2027.

Shugaban Kwamitin Zaɓen Fidda Gwani na Gwamna na PDP a jihar, Abdulmaleek Danga, ya bayyana cewa Ombugadu ya samu tikitin ne ta hanyar yarjejeniya bayan mambobin jam’iyyar suka zaɓe shi.

“An umarce ni kawai da in tabbatar da Dr. Emmanuel Ombugadu a matsayin ɗan takarar gwamna na PDP a Jihar Nasarawa na shekarar 2027, bayan mambobin jam’iyya sun zaɓe shi ta hanyar maslaha,” in ji Danga.

Ya bayyana tsarin zaɓen a matsayin wanda ya gudana cikin lumana, adalci da gaskiya, tare da ayyana Ombugadu a hukumance a matsayin ɗan takarar jam’iyyar bayan kammala zaɓen.

Da yake jawabi bayan tabbatarwar, Ombugadu ya gode wa mambobin jam’iyya da wakilan taro bisa goyon baya da amincewar da suka nuna masa, wanda ya daga matsayin sa daga mai neman takara zuwa ɗan takara.

“Da goyon bayanku, amincewarku da wannan tabbaci, kun sauya matsayinmu zuwa na ɗan takara. Ina matuƙar gode muku,” in ji shi.

Ya ce fitowarsa ta biyo bayan tattaunawa mai faɗi da dattawan jam’iyya da masu ruwa da tsaki, ciki har da kwamitin gudanarwar jam’iyyar a jihar da shugabancin jam’iyyar na ƙasa. 

A cewarsa, waɗannan tattaunawa sun samar da haɗin kai da manufa guda ga jam’iyyar a jihar.

“Idan kuka bani dama, za mu fara aiki kai tsaye. Zan fara aiki nan take domin ba mu da lokaci,” ya ƙara da cewa.

Ombugadu ya kuma yi amfani da damar wajen gabatar da abokin takararsa na 2023, Yahaya Ohinoyi, a matsayin abokin takararsa na 2027, inda ya bayyana shi a matsayin “mataimakin gwamna mai jiran gado.” Ya kuma roƙi Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta lura da wannan naɗi.

“Idan kuka bani dama, a matsayin aikina na farko, bari in gabatar da Mataimakin Gwamnan 2027. Ba kowa ba ne face Yahaya Ohinoyi, wanda zai zama
 Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa tare da mara min baya a zaɓen 2027 da yardar Allah,” in ji shi.

Ɗan takarar ya sanar da cewa jam’iyyar za ta fara rangadin ƙananan hukumomin jihar nan ba da jimawa ba domin ƙaddamar da gagarumin yaƙin neman zaɓe da nufin lashe kujerar gwamnatin jihar da ke kan titin Shendam Road.

 Ya ƙara da cewa kundin manufofin jam’iyyar na 2027 zai ginu ne kan tubalan da aka shimfiɗa a manufofin 2019 da 2023.

“Muna da cikakken kundin tsare-tsare. Sabunta shi aka yi daga na 2019 da 2023 domin dacewa da 2027,” in ji shi.

Ombugadu ya kuma sanar da cewa PDP za ta shiga zaɓen cike gurbi na Sanatan Nasarawa ta Arewa da ke tafe, inda ya tabbatar da cewa masu neman takarar jam’iyyar suna aiki domin haɗa kai da fitar da ɗan takara guda ta hanyar maslaha.

“A cikin kwanaki ashirin da wani abu masu zuwa, za mu yi zaɓen cike gurbi a Mazabar Sanatan Nasarawa ta Arewa. Jam’iyyarmu za ta shiga kuma za ta yi nasara,” ya bayyana.

Ya gode wa jami’an INEC da suka halarta tare da ƙarfafa magoya baya su ci gaba da jajircewa, yana mai cewa jam’iyyar tana nan “a cikin jerin masu takara, kuma da yardar Allah za mu zama gwamnoninku a shekarar 2027.”

Ombugadu shi ne ɗan takarar gwamna na PDP a zaɓen 2023, wanda aka fafata sosai, inda daga ƙarshe Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasarar gwamna mai ci, Abdullahi Sule.
 

No comments