Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Laraba Da Alhamis A Matsayin Ranakun Hutu Domin Bikin Babbar Sallah

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Laraba da Alhamis a matsayin ranakun hutu domin bikin Babbar Sallah (Eid ul-Adha). Ministan Harkokin Cikin Gida,...


Gwamnatin Tarayya ta ayyana Laraba da Alhamis a matsayin ranakun hutu domin bikin Babbar Sallah (Eid ul-Adha).

Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, shi ne ya ba da sanarwar hakan.

Babbar Sakatariyar ma’aikatar, Dakta Magdalene Ajani, ta bayyana a cikin wata sanarwar manema labarai cewa: “Wannan ayyana hutun yana nuna irin girmamawa mai zurfi da Gwamnatin Tarayya take yi ga addini da zukatan miliyoyin Musulman Nijeriya da ke haÉ—uwa da al’ummar Musulmi ta duniya wajen gudanar da wannan ibada mai alfarma.”

Ta ce ministan ya miÆ™a saÆ™on taya murna na gwamnati ga É—aukacin al’ummar Musulmi a Nijeriya da ma waÉ—anda suke Æ™asashen waje.

Ajani ta Æ™ara da cewa: “Eid ul-Adha biki ne mai matuÆ™ar muhimmanci a É“angaren ibada, wanda ya ginu kan darussan sadaukarwa, biyayya ga Allah, da tausayi ga ‘yan’uwa.”

Gwamnatin ta buÆ™aci É—aukacin ‘yan Nijeriya da su yi amfani da wannan lokaci wajen addu’a da yin tunani mai zurfi, tare da neman shiriyar Ubangiji ga Æ™asa yayin da take ci gaba da Æ™oÆ™arin tabbatar da zaman lafiya, tsaro, da wadata ga kowane É—an Æ™asa.

“Cikin ruhin ‘yan’uwantaka, mutuntaka ta bai É—aya, da haÉ—in kan Æ™asa, Gwamnatin Tarayya tana yi wa É—aukacin Musulmai fatan bikin cikin lumana, albarka, da farin ciki,” inji ta.
 

No comments