Hukumar kiyaye haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ta shawarci masu ababen hawa da ke amfani da babbar hanyar Abuja–Kaduna da su koma hanyar Kachia–Bwari...
Hukumar kiyaye haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ta shawarci masu ababen hawa da ke amfani da babbar hanyar Abuja–Kaduna da su koma hanyar Kachia–Bwari sakamakon tsananin cunkoso da ya turnuƙe hanyar a tsakanin Jere zuwa Katari, dalilin yawaitar zirga-zirga yayin bukukuwan Babbar Sallah.
A cikin sanarwar da Kwamandan Sashen Kaduna na hukumar, Corps Commander Andrew Longkam, ya sanya wa hannu a ranar Lahadi a Kaduna, hukumar ta bayyana cewa ayyukan gyaran hanya da ake yi, haɗe da ruwan sama mai ƙarfi da kuma yawaitar motoci, sun ƙara ta’azzara cunkoso a kan hanyar.
FRSC ta ce, babbar matsalar cunkoso tana a yankin Nasarawa Azara tsakanin Katari da Jere, inda zirga-zirga ke tafiya a sannu sakamakon cunkoso mai tsanani.
Hukumar ta kuma danganta matsalar da rashin haƙuri da rashin bin layi da wasu direbobi ke yi, lamarin da ke ƙara jinkirta tafiyar ababen hawa a hanyar.
Ta bayyana cewa ofishin FRSC na Kaduna ya tura ƙarin jami’ai zuwa wuraren da lamarin ya fi tsanani domin kula da zirga-zirga, tare da haɗin gwiwar Sojojin Nijeriya da sauran hukumomin tsaro da ababen more rayuwa.
Duk da wannan ƙoƙari, hukumar ta ce cunkoson na ci gaba da wanzuwa, inda ta yi kira ga direbobi da su kasance masu haƙuri, bin dokokin hanya da kuma yin aiki tare da jami’an da ke bakin aiki.
FRSC ta shawarci masu tafiya daga Kaduna zuwa Abuja da su yi amfani da madadin hanya ta Kachia, Maraban Kubacha, Jere, Bwari zuwa Dutse Abuja, haka kuma masu tafiya daga Abuja zuwa Kaduna su bi wannan hanya a akasin shugabanci.
Hukumar ta kuma yi gargaɗi kan kauce wa tsallake-tsallake cikin haɗari da bin hanya ta sabanin alkibla, tare da tabbatar da cewa motocinsu suna cikin yanayi mai kyau kafin su fara tafiya.
Bugu da ƙari, ta shawarci direbobi da su guji tafiye-tafiyen dare idan ba lallai ba, su riƙa bin iyakar gudu, tare da bin dukkan dokokin hanya da umarnin jami’an kula da zirga-zirga.
FRSC ta tabbatar wa jama’a cewa za ta ci gaba da ɗaukar matakai don tabbatar da tsaron rayuka, rage haɗurran hanya da kuma tabbatar da sauƙin zirga-zirga a lokacin bukukuwa da ma bayan su.
.jpg)
No comments