Daga Ibrahim Muhammad, Kano Hon. Abdurrahman Mansur Mainasara Salga ne ya lashe zaben fitar da gwani na jam’iyyar African Democratic Congres...
Hon. Abdurrahman Mansur Mainasara Salga ne ya lashe zaben fitar da gwani na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) domin tsayawa takar majalisar tarayya a Ĉaramar Hukumar Dala ta jihar Kano, bayan ya samu Ĉuri’u 8,973.
Zaben wanda aka gudanar a ranar 21 ga Mayu, 2026, ya gudana bisa tsarin Ĉato bayan Ĉato ĈarĈashin jagorancin dokar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ĉasa (INEC). 'Yan takara uku ne suka fafata: Hon. Abdurrahman Mansur Mainasara Salga, Hon. Nasir Isa, da Hon. Bashir Muhammad.
A ĈarĈashin kulawar wakilan uwar jam’iyyar ta Ĉasa, Ĉungiyoyin sa-ido da jami’an tsaro, maza da mata mambobin ADC a Dala sun fito domin kaÉa Ĉuri’ar su cikin kwanciyar hankali.
Bayan kammala zaben, kwamitin gudanarwa ya bayyana sakamakon haka: Hon. Nasir Isa ya samu kuri’u 821, Hon. Bashir Muhammad ya samu kuri’u 1,584, yayin da Hon. Amb. Abdurrahman Mansur Mainasara Salga ya zama na Éaya da Ĉuri’u 8,973 daga cikin jimillar Ĉuri’u 11,377 da aka kaÉa.
Dangane da haka, an tabbatar da Mainasara Salga a matsayin dan takar ADC na majalisar tarayya mai wakiltar Dala a zaben 2027.
Da yake jawabii kan nasarar da ya samu Hon. Mainasara Salga ya nuna godiyar sa ga mambobin jam’iyyar a Dala bisa goyon bayan da suka ba shi. Ya kuma buĈaci sauran yan takara da ya fafata da su da su hada kai domin Ĉarfafa jam’iyyar ADC domin cimma nasara a zaben 2027.

No comments