Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

APC: Na Amince Da Sakamakon Zaɓen Fidda Gwani Gwamnan Nasarawa -‘Yar Takara

Daga Zubairu Lawal, Lafia 'Yar takarar gwamnan Jihar Nasarawa a jam’iyyar APC, Dr. Fatimah Abdullahi, ta bayyana cewa ta amince da sakam...


Daga Zubairu Lawal, Lafia

'Yar takarar gwamnan Jihar Nasarawa a jam’iyyar APC, Dr. Fatimah Abdullahi, ta bayyana cewa ta amince da sakamakon zaɓen fidda gwani da jam’iyyar ta gudanar, tare da taya Sanata Ahmed Aliyu Wadada murnar lashe tikitin takarar gwamna.

Dr. Fatimah ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar bayan kammala zaɓen fidda gwani na APC, inda ta gode wa magoya bayanta bisa irin goyon baya, ƙwazo da sadaukarwar da suka nuna a lokacin kamfen.

Ta ce gwagwarmayar da suka yi ba ta tsaya kan mutum ɗaya ba ne, sai dai domin gina Jihar Nasarawa mai ƙarfi da adalci inda kowane ɗan ƙasa zai samu damar bayyana ra’ayinsa.

“Jam’iyya ta yi magana, jama’a sun yanke hukunci, kuma na amince da sakamakon zaɓen fidda gwani gaba ɗaya,” in ji ta.

Ta kuma yi kira ga dukkan magoya bayanta, masu ruwa da tsaki da sauran masu yi mata fatan alheri da su haɗa kai tare da ɗan takarar APC, Sanata Ahmed Aliyu Wadada, domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a babban zaɓen shekarar 2027.

Dr. Fatimah Abdullahi ta yi amfani da wannan dama wajen kira ga mata da su ƙara shiga harkokin siyasa da kuma neman muƙaman shugabanci.

A cewarta, lokaci ya yi da za a bai wa mata dama wajen yanke hukunci da tsara manufofin da suka shafi rayuwar al’umma, tana mai jaddada cewa idan mata suka shiga siyasa, shugabanci kan fi zama mai adalci da kula da jama’a.

Ta ƙarfafa wa mata a faɗin Jihar Nasarawa da su yi rajista, su shiga siyasa, su tsaya takara tare da mara wa masu neman shugabanci baya domin gina makoma mai kyau ga jihar.

A ƙarshe, ta jaddada cewa har yanzu tana nan daram a cikin jam’iyyar APC kuma za ta ci gaba da bayar da gudunmawa domin ganin jam’iyyar ta samu nasara a dukkan matakai.
 

No comments