Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

CBN Ya Ƙaddamar Da Sabon Kundin Dokokin Canjin Kuɗaɗen Waje

Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya ƙaddamar da bugu na huɗu na kundin dokokin canjin kuɗaɗen waje, wanda aka ƙaddamar a ranar Juma’a. An tsara...

Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya ƙaddamar da bugu na huɗu na kundin dokokin canjin
kuɗaɗen waje, wanda aka ƙaddamar a ranar Juma’a.

An tsara shi ne domin ya fara aiki daga ranar 1 ga Yuni, 2026, a matsayin wani ɓangare na gyare-gyaren da ake ci gaba da yi domin inganta gaskiya, yawaitar kuɗi a kasuwa da kuma ƙarfafa amincewa da kasuwar canjin kuɗaɗen waje ta Nijeriya.

Da yake jawabi yayin ƙaddamar da sabon kundin a Abuja, Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Olayemi Cardoso, ya ce wannan mataki yana nuna jajircewar CBN wajen ƙarfafa ginshiƙan tattalin arzikin ƙasa da kuma sabunta tsarin gudanar da harkokin canjin kuɗaɗen waje a Nijeriya.

“Wannan ƙaddamarwa tana nuna haɗin kan mu wajen ƙarfafa tushen tattalin arzikin Nijeriya, inganta gaskiya da kuma ƙarfafa amincewa da kasuwar canjin kuɗaɗen waje,” inji Cardoso.

Ya ci gaba cewa sabunta kundin ya zama wajibi sakamakon sauyin tattalin arzikin duniya, gyare-gyaren cikin gida, da kuma sauyin da ake ci gaba da yi a kasuwar canjin kuɗaɗen waje ta Nijeriya.

“A cikin shekaru goma da suka gabata, tattalin arzikin duniya ya ƙara zama mai rikitarwa da rashin tabbas, yayin da tattalin arzikin cikin gida ya samu sauye-sauye, ciki har da ƙoƙarin faɗaɗa hanyoyin samun kuɗaɗen waje da kuma shawo kan matsin hauhawar farashi."

Cardoso ya ƙara da cewa, “An samar da wannan bugu na huɗu ne bayan dogon nazari da tattaunawa da masana, tare da daidaita shi da ƙa’idojin duniya. Wannan yana nuna ƙudurin mu na sabunta tsarin gudanar da canjin kuɗaɗen waje domin samar da karin haske, daidaito da ingancin kasuwa. Kundin zai fara aiki daga ranar 1 ga Yuni, 2026.”

Gwamnan na CBN ya ce nasarar aiwatar da sabon tsarin za ta dogara ne da haɗin kan bankunan canjin kuɗaɗen waje, kamfanoni, hukumomi, ma’aikatu, masu fitar da kaya ƙasashen waje, masu shigo da kaya daga ƙasashen waje da sauran masu ruwa da tsaki.

“Bin wannan tsari yana da muhimmanci, haɗin kan ku wajibi ne, kuma haɗin gwiwarku shi ne ginshiƙin ɗorewa da amincin kasuwar canjin kuɗaɗen waje ta Nijeriya,” inji Cardoso.

Ya ƙara da cewa CBN zai ƙarfafa tsarin sa-ido domin tabbatar da adalci, ɗaukar alhaki da bin ƙa’idoji a kasuwar canjin kuɗaɗen waje.

“Domin tabbatar da sauƙin amfani da wannan kundin, za a samar da shi kyauta ga dillalan da aka amince da su, domin fifita bin doka maimakon neman kuɗin sayarwa,” inji Cardoso.

A nasa jawabin, Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Nijeriya mai kula da Sashen Manufofin Tattalin Arziki, Muhammad Abdullahi, ya ce sabon kundin wani ɓangare ne na manyan gyare-gyaren da aka fara ƙarƙashin jagorancin Cardoso, domin dawo da amincewa, ƙara gaskiya, zurfafa yawaitar kuɗi da kuma ƙarfafa ingancin kasuwa.

Abdullahi ya ce an yi wannan gyara ne domin daidaita tsarin canjin kuɗaɗen waje na Nijeriya da halin da kasuwa ke ciki yanzu da kuma ƙa’idojin duniya.

“Sabon kundin da muke ƙaddamarwa a yau ba wani tsari ne dabam ba, sai dai wani ɓangare ne na manyan gyare-gyaren hukumomi da aka tsara domin ƙarfafa gaskiya, amincewa da ingancin tsarin canjin kuɗaɗen waje na Nijeriya,” Cewar Abdullahi.

A cewar sa, an samar da kundin ne bayan tattaunawa mai zurfi da bankunan masu kuɗaɗen waje, masu fitar da kaya, kamfanoni, hukumomi, abokan hulɗar ci gaba da sauran masu ruwa da tsaki daga gwamnati da kamfanoni masu zaman kan su.

Ya ce tsarin bitar ya mayar da hankali kan sauƙaƙa harkokin kasuwanci domin rage tsaiko, matsalolin aiki da ruɗanin kasuwa. “Burin su shi ne rage cikas a harkokin mu’amala, inganta saurin gudanar da ayyuka, ƙarfafa amincewa a kasuwa, jawo mutane su yi amfani da kasuwa ta hukuma, da samar da sauƙin amfani ga halattattun masu amfani da kasuwar canjin kuɗaɗen waje ta Nijeriya,” inji shi.

Abdullahi ya bayyana cewa sabon kundin ya kawo manyan sauye-sauye, ciki har da daidaita tsarin canjin kuɗin matafiya ƙasashen waje (PTA) da na BTA da sabbin ƙa’idojin canjin kuɗi ga 'Bureau De Change'.

A ƙarƙashin sabon tsarin: Kashi 75 cikin 100 na PTA da BTA za a biya su ta hanyar tsarin aika saƙon kuɗi ta zamami. Kashi 25 cikin 100 kuma za a iya biya da kuɗi a hannu, wato wuri na gugar wuri.

Sauran sauye-sauyen sun haɗa da: Ƙara yawan kuɗin da za a iya biya kafin shigo da kaya daga kashi 15 zuwa kashi 30. Sai samar da Fam Lamba NXP kyauta.

Akwai kuma samar da sabbin tanade-tanade kan:
fitar da ayyuka zuwa ƙasashen waje, mu’amalolin PAPSS, tura kuɗaɗe daga kamfanonin fasaha,
da asusun jarin masu zuba jari waɗanda ba mazauna ƙasa ba ne.

Kundin ya kuma samar da damar biyan kuɗin wasu ayyuka, kuɗaɗe da cajin da ake samu a kuɗin waje da irin wannan kuɗin waje, tare da biyan kuɗin makaranta na jami’o’i da na digiri na gaba a ƙasashen waje har zuwa dala 25,000 a kowanne zangon karatu.

Haka nan Abdullahi ya ƙara da cewa sabon tsarin ya tanadi: cikakkiyar damar amfani da kuɗin asusun ajiya na yau da kullum da kuɗin fitar da kaya, damar kamfanonin ƙasashen waje masu aiki a ɓangaren albarkatun ƙasa su mayar da kashi 100 cikin 100 na kuɗin fitar da kayan su, da cire wajabcin amfani da 'Form A' wajen aika kuɗi ta asusun ajiya na yau da kullum.

“Waɗannan gyare-gyare gaba ɗaya suna da nufin inganta ingancin aiki, ƙarfafa amincewa a kasuwa, rage cikas na gudanarwa, tallafa wa halattattun harkokin kasuwanci, ƙarfafa bin ƙa’idoji da kuma sabunta tsarin canjin kuɗaɗen waje na Nijeriya,” cewar sa.
 

No comments