Rundunar sojin haɗin gwiwa ta Operation Haɗin Kai (OPHK) da ke lura da shiyya ta biyu, ta yi nasarar fatattakar wani gagarumin hari da ’yan...
Rundunar sojin haɗin gwiwa ta Operation Haɗin Kai (OPHK) da ke lura da shiyya ta biyu, ta yi nasarar fatattakar wani gagarumin hari da ’yan ta’adda suka kai yankin Kukareta da ke Arewa maso Gabashin ƙasar nan a daren Laraba wayewar Alhamis.
Harin, wanda aka fara shi jim kaɗan bayan tsakar dare zuwa misalin karfe 3:00 na asuba, ya gamu da tirjiya daga dakarun soji waɗanda suka yi martani, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa bayan sun tafka asara mai yawa.
A cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Kanar Sani Uba ya fitar a ranar 23 ga watan Afrilu, 2026, ya bayyana cewa sojoji sun yi nasarar kashe ’yan ta’adda 24 a yayin artabun.
Haka kuma, binciken da sojoji suka gudanar a fagen daga bayan ƙura ta lafa ya kai ga gano ɗimbin makaman da ’yan ta’addan suka bari, waɗanda suka haɗa da Bindigogi kirar AK-47 guda 18 da wasu manyan bindigogi na GPMG guda 3, Bindigogin kakkabo jiragen sama (PKT) guda 2 da bututun harba bama-bamai na RPG guda 3 da na Mortar guda 2, Guruneti (Hand grenades) guda 4 da kuma dimbin alburusai.
Sanarwar ta kara da cewa sojoji biyu ne suka samu raunuka a lokacin musayar wuta, kuma tuni aka duba lafiyarsu inda suke cikin yanayi mai kyau. Kazalika, wata motar yaki ta sojoji (Tank) guda ɗaya ta samu matsala bayan tayoyinta sun fashe a lokacin da take kai dauki.
A halin yanzu, sojoji na ci gaba da bin sawun ’yan ta’addan da suka tsere da raunuka, inda aka ga alamun jini da kayayyakin magunguna a hanyoyin da suka bi yayin gudun ceton rai.
Wannan nasara dai ta ƙara tabbatar da irin shirin da dakarun soji suke da shi na murƙushe duk wani yunƙuri na ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas, inda rundunar ta lashi takobin ci gaba da matsa lamba har sai ta kawo ƙarshen ayyukan ta'addanci a yankin baki ɗaya.


No comments