Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Matasa Sun Yi Gangamin Goyon Bayan Mataimakin Gwamna Don Takarar Sanatan Nasarawa

  Daga Zubairu Lawal, Lafia Tawagar haɗin gwiwar ƙungiyoyin matasa daga yankin Nasarawa Ta Kudu a Jihar Nasarawa ta sake jaddada goyon bayan...

 
Daga Zubairu Lawal, Lafia

Tawagar haɗin gwiwar ƙungiyoyin matasa daga yankin Nasarawa Ta Kudu a Jihar Nasarawa ta sake jaddada goyon bayan ta ga Dakta Emmanuel Akabe, Mataimakin Gwamnan Jihar, domin tsayawa takarar kujerar Majalisar Dattawa ta yankin a shekarar 2027.

Ƙungiyar ta bayyana Emmanuel Akabe,  mataimakin Gwamna, shi ne mafi cancanta kuma ƙwararren mutum da ya dace da wannan kujera a 2027.

Shugaban ƙungiyar, Malam Abimiku Dangana, ne ya bayyana goyon bayan matasan a yayin taron manema labarai da aka gudanar a Lafia ranar Alhamis.

Dangana ya ce ƙungiyar za ta fara tattara goyon baya domin tabbatar da nasarar Akabe a 2027.

A cewar sa, “Muna so mu bayyana aniyarmu ta zagaya ƙananan hukumomi biyar da suka ƙunshi wannan yankin sanata domin tara goyon baya da zai kai Akabe Majalisar Dattawa a 2027.”

“Mu, a matsayin haɗin gwiwar ƙungiyoyin matasa daga Nasarawa Ta Kudu, mun kira wannan taron manema labarai ne domin bayyana matsayar mu kan makomar siyasar yankinmu.

“Bayan dogon nazari, tuntuba mai zurfi, da kuma la’akari da yanayin siyasa da kuma halayen jagoranci, muna bayyana goyon bayanmu ba tare da ja da baya ba ga Mai Girma Dakta Emmanuel Agbadu Akabe, Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa na yanzu, domin wakiltar yankin Nasarawa Ta Kudu a Majalisar Dattawa a 2027.

Wannan ba kawai magana ta siyasa ba ce, yana nuna burin matasan yankin mu na samun shugabanci mai hangen nesa, ci gaba mai dorewa da kuma wakilci mai inganci.”

Dangana ya ƙara da cewa Akabe mutum ne mai kyawawan halaye, basira da kuma ƙwarewa da aka tabbatar.

Ya ce, “Baya ga ƙwarewar sa a fannin lafiya, Dakta Akabe ya nuna ƙwarewa ta musamman a harkokin shugabanci da gudanarwa. 

"Ya bayar da gudummawa sosai kuma har yanzu yana ci gaba da bayarwa wajen ci gaba da zaman lafiyar jihar.

“Yana da tarihin aiki mai kyau, gogewa mai yawa, fahimta mai zurfi game da yankin Nasarawa Ta Kudu, salon aiki na natsuwa da fasaha, amincewa a matakin ƙasa da kuma kusanci da matasa,” in ji shi."

Shugaban ƙungiyar ya yi kira ga al’ummar yankin sanata da su haɗa kai su mara wa Akabe baya domin samun nasara a 2027.

Haka kuma, ya buƙaci jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da ta lura da gudummawar da Akabe ya bayar tare da ba shi dama domin ya yi wa al’umma hidima a matakin majalisa mafi girma.

“Mu haɗa kai domin tabbatar da cewa jagora irin Dakta Akabe, mai ɗimbin gogewa da gudummawa, ya wakilci Nasarawa Ta Kudu a Majalisar Dattawa a 2027.
 

No comments