Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

SHIRIN GYARAN HALI A KADUNA: Kwamishina Ta Buƙaci Matasa Su Mayar Da Hankali Kan Kyawawan Ɗabi'u

A wani muhimmin biki da ya gudana a ranar Laraba a jihar Kaduna, an yaye yara 45 da suka amfana daga shirin ‘Children Diversion Programme’, ...

A wani muhimmin biki da ya gudana a ranar Laraba a jihar Kaduna, an yaye yara 45 da suka amfana daga shirin ‘Children Diversion Programme’, wanda ke nufin karkatar da matasa daga munanan halaye zuwa rayuwa mai ma’ana.

Kwamishinar Harkokin Mata da Ci gaban Jama’a ta jihar Kaduna, Dakta Rabi Salisu, ita ce ta jagoranci bikin yaye yaran da aka gudanar a cibiyar kula da mata da yara da ke titin Katuru a Kaduna.

Dr Rabi ta bayyana bikin a matsayin lokaci na farin ciki da gamsuwa, tana mai cewa wannan nasara ba ƙarshen tafiya ba ce, illa dai sabon farawa ga rayuwar yaran.

Ta yaba wa yaran bisa jajircewarsu da yadda suka rungumi sauyi, tana mai cewa shirin na da manufar gyara rayuwar matasa tare da mayar da su ‘yan ƙasa nagari masu amfani ga al’umma.

“Wannan shiri yana taimakawa wajen kawar da matasa daga munanan tasiri tare da jagorantar su zuwa zama masu anfani ga al’umma. Mun yi imani cewa kowanne yaro, komai kuskuren da ya yi a baya, yana da damar samun wata sabuwar rayuwa,” in ji ta.

Dakta Salisu ta kuma jaddada cewa gwamnatin jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Gwamna Sanata Uba Sani na ci gaba da mai da hankali wajen bunƙasa jari na ɗan Adam da kuma kare masu rauni, musamman mata da yara. Ta ce shirin ya ta’allaƙa ne kan gyaran hali da sake shigar da yara cikin al’umma maimakon hukunta su.

Ta yi kira kai tsaye ga yaran da aka yaye da su ɗauki wannan rana a matsayin sabuwar mafari, tana mai jaddada cewa ilimi da horon da suka samu zai zama ginshiƙin gina kyakkyawar makoma.

Ta kuma gode wa ƙungiyoyi da abokan hulɗa da suka taimaka wajen nasarar shirin, ciki har da UNICEF da kwamitin kula da shari’ar yara, tare da ma’aikata da masu horaswa.

A ƙarshe, kwamishinar ta buƙaci iyaye da masu kula da yara da su ci gaba da ba su goyon baya yayin da suke komawa cikin al’umma, tana mai cewa cigaban yaro na nufin cigaban al’umma baki ɗaya.
 

No comments