Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Aikin Samar Da Lantarki Ta Hasken Rana (Solar) Na Naira Biliyan 3.8 a Jami’ar ADUSTECH Da Ke Kano

Gwamnatin Tarayya, ta hannun Hukumar Makamashi ta ƙasa (ECN), ta ƙaddamar da aikin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana (Solar)...


Gwamnatin Tarayya, ta hannun Hukumar Makamashi ta ƙasa (ECN), ta ƙaddamar da aikin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana (Solar) mai ƙarfin megawatt biyu (2MW) a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Ɗangote (ADUSTECH) da ke Wudil a Jihar Kano.

Wannan aiki, wanda kuɗinsa ya kai naira biliyan 3.8, yana ƙarƙashin shirin nan na 'Renewed Hope Solarization' na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Baya ga aikin samar da wutar, an kuma ƙaddamar da fitilun kan hanya guda 200 masu amfani da hasken rana a cikin harabar jami’ar.

Darakta Janar na hukumar, Dr. Mustapha Abdullahi, tare da Ministan Ƙirƙira, Kimiyya da Fasaha, Kingsley Tochukwu-Udeh, ne suka kaddamar da fara aikin a ranar Juma’a.

Dr. Abdullahi ya bayyana cewa an ba kamfanin da zai gudanar da aikin wa'adin watanni uku kacal domin kammalawa. Ya ce an tsara wannan aiki ne domin kawo ƙarshen matsalar tsadar wutar lantarki da jami’ar ke fuskanta, inda take biyan naira miliyan 22.4 a kowane wata.

"Wannan aiki na Wudil yana bin sahu ne bayan makamancinsa da muka ƙaddamar a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano a watan Satumban 2025, inda ake sanya tsarin megawatt hudu (4MW), da kuma aikin da muka ƙaddamar a Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) a makon jiya," in ji Dr. Abdullahi.

Ya ƙara da cewa an ba kamfanin Safiatu Global Resources Limited kwangilar a kan kuɗi naira biliyan 3.8, kuma ba za a kara ko sisi a kan kuɗin ba, sannan dole ne su kammala a cikin lokaci.

Binciken da hukumar ta gudanar ya nuna cewa jami’ar tana da dalibai da ma’aikata sama da 24,000, kuma buƙatar wutar da take da ita ta kai tsakanin megawatt 12.3 zuwa 16.4. Sai dai, wutar da take samu daga kamfanonin rarraba wuta ba ta taka kara ta karya ba, yayin da janaretocin da take amfani da su ba sa iya ɗaukar nauyin buƙatar jami’ar.

A nasa jawabin, Ministan Ƙirƙira, Kimiyya da Fasaha, Kingsley Tochukwu-Udeh, ya ce wannan aiki mataki ne na raya kasa a ƙarƙashin manufofin gwamnatin Tinubu na bunƙasa ilimi da ƙirƙire-ƙirƙire ta hanyar samar da ingantaccen makamashi.

Shi ma a nasa bangaren, Shugaban Jami’ar, Farfesa Musa Tukur-Yakasai, ya nuna jin daɗinsa da wannan gagarumin tallafi, inda ya ce wannan mataki zai kara bunkasa harkar bincike da koyarwa a jami’ar.

 

No comments