Wannan labari ya daɗe yana yawo a kafofin sada zumunta, amma yana da muhimmanci mu raba tsakanin gaskiya da kuma jita-jita. 1. Shin akwai...
1. Shin akwai Harajin "Saka Solar" a Gida?
A halin yanzu, babu wata doka a hukumance daga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta ce duk wanda ya sayi solar zai rinka biyan haraji na musamman don kawai yana amfani da ita a gidansa. Gwamnati ba ta bukatar talaka ya nemi izini kafin ya sayi solar.
2. Daga Ina Labarin Ya fito?
Abin da mutane suke tattaunawa akai ya samo asali ne daga wasu tsare-tsare na Hukumar Kula da Lantarki (NERC) da kuma dokokin jihohi, amma sun shafi wadannan rukunonin:
● kamfanoni da masana'antu masu manyan injina (Industrial/Commercial): Wadanda ke amfani da manyan solar masu karfin gaske (kamar wadanda suka haura MegaWatt 1). Dokar kasa ta bukaci irin wadannan su yi rajista kafin dasa lantarki.
● Hadin gwiwa da Wajen samar da lantarki (Net Metering): Idan kana so ka hada solarka da wayoyin lantarki na gwamnati ta yadda idan kana da ragowar wuta, zaka sayar wa gwamnati, to dole a saka maka mita kuma akwai ka'idoji.
● Harajin Kayayyaki (Import Duty): Akwai ƙorafe-ƙorafe kan ƙarin kuɗin shigo da kaya (customs duty) ga masu shigo da batir da fanel na solar daga kasashen waje. Wannan yana sa farashin solar ya yi tsada, amma ba wai haraji ne bayan an riga an saka ta a gida ba. Akwai sashe da ya kawo batu kan Import Adjustment Tax (IAT) wanda gwamnati ta sanya sabbin haraji kan wasu rukunin kayayyaki (tariff lines) guda 192 da ake shigowa da su daga waje don kare masana'antun gida da ke samar da irin su. Wannan ya shafi wasu sassa na na'urorin lantarki da suka hada da kayan Solar.
Idan kai mutum ne da kake son saka solar a gidanka don hasken ɗaki, fanka, ko kallon TV da sauran buƙatun gida, babu wani haraji da aka shimfiɗa maka, kuma ba kwa buƙatar izinin kowa.
Labarin da ake ji yawanci ƙarin gishiri ne na siyasa ko kuma rashin fahimtar dokar da ta shafi manyan kamfanoni.

No comments