Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

TAWAGAR TINUBU A LANDAN: Yadda Gwamnan CBN Ya Bayyana Inganci, Ƙarfi Da Juriyar Sauye-sauyen Manufofin Kuɗi A Nijeriya, Gaban Mahalarta Taron Africa Capital Forum

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ya jaddada cewa sauye-sauyen manufofin kuɗi a Nijeriya sun ƙarfafa juriya ga girgizar...




Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ya jaddada cewa sauye-sauyen manufofin kuɗi a Nijeriya sun ƙarfafa juriya ga girgizar tattalin arziki, sun kuma dawo da amincewar masu zuba jari a cikin Nijeriya, tun bayan hawa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.


Cardoso ya ce sabbin sauye-sauyen manufofin kuɗi da na fannin banki da aka aiwatar a Nijeriya sun ƙarfafa ikon ƙasar na jure wa girgizar tattalin arziki daga waje tare da dawo da amincewa a tattalin arzikin ƙasar.

Da yake jawabi a taron Africa Capital Forum da aka gudanar a birnin Landan a ranar Talata, a gefen ziyarar aiki ta Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zuwa ƙasar Birtaniya, Cardoso ya shaida wa masu zuba jari da abokan hulɗar raya ƙasa cewa Babban Bankin ya “gina tsari mai ɗorewa na jure girgiza” ta hanyar tsauraran manufofi da gyare-gyaren hukumomi.

A cewar sa, kasuwar canjin kuɗaɗen waje ta Nijeriya yanzu tana da ƙarin gaskiya da wadataccen ruwa, inda sabon tsarin musayar kudaden waje ya kawar da yawancin tsofaffin takunkuman sarrafa kuɗaɗen waje tare da sauƙaƙa harkokin kasuwanci da zuba jari.

Cardoso ya ci gaba da bayyana cewa an samu gagarumin ci gaba a shirin ƙara ƙarfin jarin bankuna , inda sama da bankuna 30 suka riga suka cika sabbin ƙa’idojin jarin, yayin da ake ci gaba da tantance sauran. Ya ce, “kimanin kashi 28 cikin 100 na jarin da aka samu a wannan shiri ya fito ne daga ƙasashen waje,” yana mai ƙarawa da cewa hakan alama ce ta sabuwar amincewa da daidaiton tsarin kuɗi na Nijeriya.

Ya kuma bayyana cewa kuɗaɗen da ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje ke aikowa gida sun ƙaru sosai, lamarin da ya taimaka wajen faɗaɗa hanyoyin samun kuɗaɗen waje, tare da ƙarfafa ajiyar kuɗin ƙasar domin jure sauye-sauyen tattalin arzikin duniya.

Ya ce, “abin da muka sa a gaba shi ne kare wannan daidaito da muka samu da wahala domin masu zuba jari da masu ruwa da tsaki su samu damar tsara harkokinsu cikin kwanciyar hankali.”

Ya ƙara da cewa a ƙarƙashin jagorancin sa, CBN zai ci gaba da kasancewa, mai buɗe ido da gaskiya, yana bayar da bayanai akai-akai, tare da ɗaga matakin tsammanin jama’a domin kauce wa kura-kuran da suka gabata.

Cardoso ya tabbatar da cewa hauhawar farashin kayayyaki ya ragu sosai, kwanciyar hankali a farashin canjin kuɗi ya inganta, kuma sauye-sauyen da aka yi sun sanya tattalin arzikin Nijeriya “a hanya mai kyau ta samun babban ci gaba wanda zuba jari na cikin gida, gyare-gyaren fannin mai, da kuma sabuwar amincewa daga duniya za su jagoranta.”

Ya ce, “za mu ci gaba da tabbatar da daidaito, ba kawai wajen rage hauhawar farashi ba, har ma a kasuwar canjin kuɗi, tare da ƙarin gaskiya da rahotanni masu ɗorewa.”
 

 

No comments