Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Hon. Haruna Kabiru Ya Taya Sabbin Shugabannin Jam'iyyar APC Na Kano Murna

Daga Ibrahim  Muhammad, Kano Jam'iyyar APC  ta gudanar da zaben shugabannin ta tun daga kan mazabu, Ƙananan Hukumomi da jiha cikin kwanc...

Daga Ibrahim  Muhammad, Kano
Jam'iyyar APC  ta gudanar da zaben shugabannin ta tun daga kan mazabu, Ƙananan Hukumomi da jiha cikin kwanciyar hankali da kowa ya amince, tare da yin farin ciki da yadda aka gudanar da shi cikin nasara.

Fitaccen ɗan siyasa, wanda ya yi takarar neman ɗan Majalisar tarayya a zaben 2023 daga Ƙaramar Hukumar Fagge, kuma jigo a jam'iyyar APC, Hon.Haruna Kabiru Wakili ne ya bayyana taya murnar sa ga sabbin shugabannin.

Hon. Wakil ya bayyana haka ne a wata zantawa da ya yi da manema labarai a Kano. Sannan ya yi godiya ga jagororin jam'iyyar na Jihar Kano, musamman wanda ya zama  babban jagoranta, Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da  tsohon Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da mataimakin shugaban  majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin bisa haɗa kai da suka yi aka samun wannan nasara.

Daga nan ya yi nuni da cewa tsohon Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Barau I. Jibrin su aka zo aka samu a jam'iyyar suna ɗawainiya da ita, musamman Sanata Barau.I jibrin, ya ɗauki nauyin ci gaban jam'iyyar a dukkan Ƙananan Hukumomi 44 na jihar Kano, babu dare ba rana.

Hon. Haruna Kabiru Wakili  ya ƙara da cewa  ganin an sami ƙaruwa na shigowar Gwamnan jihar Kano cikin jam'iyyar, tunda ya shigo da Gwamnati da jama'ar sa, Sanata Barau.I Jibrin ya ce duk ƙudurin da yake da shi ya janye, "muna yi masa godiya na wannan dattaku da ya nuna," in ji Hon. Wakil.

Hon. Haruna Kabiru Wakili ya yi kira ga 'yan jam'iyyar su yi ƙoƙarin tafiya tare cikin haɗin kai, musamman ganin yanzu an zabi sabbin shugabannin jam'iyyar cikin haɗin kai ba tare da rigima ba, suna fata nan gaba idan an zo fitar da 'yan takara, duk wanda Allah ya bai wa nasara a bi shi, wanda bai samu ba ya yi haƙuri ya san cewa lokacin sa ne bai yi ba.

Ya ƙara jaddada kira ga magoya bayan jam'iyyar APC da masu neman matsayi daban-daban a cikin ta, kowa idan ya yi haƙuri akwai matsayi da aka tanadar da kowa zai amfana. Don haka suna fata zabuka da za su zona 2027, Allah zai ba su nasara su lashe dukkan kujeru da tabbatar da nasara a kowane mataki na jaha da kasa baki daya.

No comments