Yayin da saura makonni uku wa'adin ƙarfafa jarin bankuna da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya gindaya su cika, yanzu kuma CBN ya umarci ...
Yayin da saura makonni uku wa'adin ƙarfafa jarin bankuna da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya gindaya su cika, yanzu kuma CBN ya umarci dukkan bankunan kasuwanci su yi gwajin ƙarfin juriyar matsin tattalin arziki, wato 'stress test'.
Wannan umarni ya zo ne yayin da yake ci gaba da sa-ido kan tsarin bankunan domin gano yiwuwar rauni a cikin su.
An fito da wannan umarni ne a cikin wata wasiƙa da jaridar TheCable ta ruwaito cewa ta gani a ranar Asabar.
Wasiƙar dai an aika ta ga dukkan bankuna, kuma tana ɗauke da umarnin ne a ranar 6 ga Maris, 2026.
Wannan rana dai kuma ita ce ranar da CBN ya sanar cewa tsarin bankunan Nijeriya yana nan cikin kwanciyar hankali kuma yana da ƙarfi.
Wannan sabon umarni na mai kula da bankuna ya zo ne a daidai lokacin da bankuna ke cikin shirin ƙara jarin su, yayin da wa’adin ranar 31 ga Maris, 2026 da CBN ya sanya ke gabatowa.
Menene Gwajin Jure Matsin Tattalin Arziki?
Gwajin dai wata hanya ce da ake amfani da ita domin auna yadda banki zai iya jure matsanancin yanayin tattalin arziki, kamar irin su
tsananin durƙushewar tattalin arziki,
faɗuwar kasuwanni
ko wasu nau'ukan tangal-tangal da girgiza tattalin arziki.
Dalilin Umarnin CBN:
A cikin wasiƙar, CBN ya ce wannan umarni ya yi daidai da tanadin dokar da 'Banks and Other Financial Institutions Act (BOFIA) ta 2020, musamman sashe na 13 da na 63, waɗanda suka tanadi cewa bankuna dole su riƙa riƙe jari mai isasshen ƙarfi domin rufe duk wata barazana da haɗurran da ke tattare da ayyukan su.
CBN ya kuma ce wannan umarni bai sauya ƙa’idojin gwajin da aka fitar a Maris 2019 ba.
Abubuwan Da CBN Ya Umarci Bankuna Su Gwada
CBN ya umarci bankuna su gwada yadda kundin jimillar bashin su zai iya jure matsin tattalin arziki cikin watanni 12.
Za su yi hakan ta hanyar kwaikwayon abubuwa da suka haɗa da lalacewar ingancin kadarori, haɗarin shugabanci da gudanarwa, faɗuwar farashin kayayyaki a kasuwa, motsin hawa da saukar farashin canjin kuɗi a kasuwar musayar kuɗaɗen waje, canje-canje a kasuwannin kamfanonin da suka karɓi bashi, tangarɗar tsarin samar da kayayyaki, sai kuma raguwar buƙatar kayayyaki.
Abubuwan Da za Da Za A Tantance
Gwajin zai tantance tasirin waɗannan abubuwa ga a kan sikelin bashin da ba a biya ba, wato a Turance 'Non-Performing Loans – NPLs', adadin tanadin asarar bashi, da kuma wadatar jari na banki.
Yayin gwajin, CBN ya umarci bankuna su haɗa da
dukkan bashin da ke cikin littafin su,bashin da ba a rubuta kai tsaye ba, sai kuma bashin da ya shafi daraktoci ko ma’aikatan ciki.
Haka kuma dole ne su yi hasashen cewa dangane da wasu basussukan za su matsa wa zuwa mataki mafi haɗari bisa ƙa’idodin PG da CBN ya gindaya.
Dangane da buƙatar ƙarin jari idan aka samu giɓin jari, CBN ya ce idan sakamakon gwajin ya nuna cewa banki yana da giɓin jari, to dole bankin ya
tara kashi 100% na giɓin jarin da gwajin bankin ya nuna, ko kuma kashi 50% na giɓin da CBN ya lissafa, wato duk wanda ya fi yawa a tsakanin biyun. Kuma za a baiwa bankin watanni 18 domin cike wannan giɓin jari.
Bayan haka, wannan sabon matakin jari zai zama sabuwar buƙatar jarin bankin bisa barazanar haɗarin da ka iya afkawa kan jarin banki, har zuwa zagayen gwaji na gaba.
Daga nan CBN ya umurci bankuna su miƙa rahoton wannan gwajin da kwamitin gudanarwar su zai amince da shi kafin ƙarshen aiki a ranar 30 ga Afrilu.
Idan kuma banki bai nuna giɓin jari ba bayan gwajin, to za a ci gaba da yin wannan gwajin duk bayan watanni 12.

No comments