1. Alama ta farko ita ce yadda tun bayan karyewar tsadar farashin kayan abinci a tsakiyar 2025, har yau farashin kayan gona bai ƙara yin t...
2. Yadda malejin tsadar rayuwa ya yi ƙasa zuwa kashi 15.1 ya nuna kayan abinci da kayan masarufi ba su tashi fiye da ƙarfin buƙatun mai ƙaramin ƙarfi ba.
3. Ci gaba da samun daidaiton daraja da tagomashin Naira a kasuwar canjin kuɗaɗen waje na ƙara wa tattalin arziki ƙwarin guiwa tare da samun ƙarin yawan kuɗaɗen waje daga masu sha'awar zuba jari da 'yan ƙasa mazauna ƙasashen waje.
4. Yadda Asusun Ajiyar Kuɗaɗen Waje a CBN ya cika maƙil da kusan Dala biliyan 50 zuwa cikin watan Fabrairu, ya ƙara nuna samun ci gaba da ake yi, bisa la'akari da cewa wannan gwamnati Dala biliyan 3 da kaɗan kacal ta gada a asusun a ƙarshen Mayu, 2026.
5. Shirin Ƙarfafa Jarin Bankuna da CBN ya tilasta bankunan Nijeriya ya tabbatar da ƙarin ƙarfin tattalin arziki a farkon 2026. Zuwa yanzu bankunan da suka cika sharuɗɗa na da jimillar ƙarfin jari fiye da Naira tiriliyan 4.5, yayin da ake sa ran su kai Naira tiriliyan 6 nan zuwa ƙarshen watan Maris, lokacin da wa'adin da CBN ya ba su zai cika.
6. Rage adadin kuɗin ruwa daga kashi 27% bisa 100% zuwa kashi 26.5 bisa 100%, zai rage tsadar karɓar lamuni daga hannun bankuna.
6. Yadda gundarin adadin ajiyar kuɗaɗen waje na Nijeriya ya kai har Dala biliyan 34.80 a ƙarshen 2025, daga Dala biliyan 3.99 a Mayu 2023, ya nuna ƙarfin tattalin arzikin Nijeriya na kan miƙaƙƙar hanyar tabbatar da ƙudirin kaiwa darajar Dala Tiriliyan Ɗaya nan zuwa shekarar 2030.
No comments