Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Dakarun Nijeriya Sun Kashe 'Yan Ta'adda 61 A Malam Fatori Da Ke Arewa Maso Gabashin Ƙasar Nan

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne yayin da 'yan'taddan suka yi ƙoƙarin shige sansanin sojin da ke garin Malam Fatori a jihar Borno...


Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne yayin da 'yan'taddan suka yi ƙoƙarin shige sansanin sojin da ke garin Malam Fatori a jihar Borno dake arewa maso gabashin Nijeriya

Rahotanni  na cewa sojin ƙasa da na saman Nijeriya sun yi nasarar kashe ‘yanta’adda aƙalla 61 a garin Malam Fatori da ke jihar Borno a arewa maso gabas.

Wani rahoton da Zagazola Makama ya fitar wanda babban mai bai wa Shugaba Tinubu shawara na musamman kan dabaru da watsa labarai, Bayo Onanuga, ya wallafa a shafinsa na X, ya ce lamarin ya auku ne a lokacin ‘yanta’addan suka nemi kutsawa cikin sansanin soji a Malam Fatori da ke ƙaramar hukumar Abadam ta jihar Borno.

Rahoton ya ambato majiyoyin tsaro suna cewa ‘yanta’addan sun ƙaddamar da harin da sanyin safiyar Laraba ne inda suka nufi sansanin sojin da ƙafa kuma suka yi amfani da jirage mara matuƙa a wani yunƙuri na karya katangar sansanin sojin da ƙarfin hali.

Sai dai martani mai ƙarfi na haɗin gwiwa da dakarun ƙasa da na sama suka yi ya fi ƙarfin ‘yanta’addan.

Kazalika wata sanarwar da daraktan hulɗa da jama’a da watsa labarai na rundunar sojin saman Nijeriya, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya fitar kuma Usman Kuka Sheka tsohon kakakin sojin Nijeriya ya wallafa a shafinsa na Fabeook, ta tabbatar da aikin da sojin saman ta yi a Malam Fatori.

“Aikin na haɗin gwiwa ya yi nasarar hana masu tayar da ƙayar bayan karya katangun tsaro, lamarin da ya ƙarfafa ƙoƙarin da ake yi na daidaita lammura a garuruwan da ke kan iyakoki,“ in ji sanarwar.
 

No comments