Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya sanar da cewa zai bayar da dala biliyan 10 daga dukiyarsa ta ƙashin kansa domin kafa wata sabuwar ƙu...
Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya sanar da cewa zai bayar da dala biliyan 10 daga dukiyarsa ta ƙashin kansa domin kafa wata sabuwar ƙungiya ta duniya mai suna “Board of Peace”, wadda ya ce za ta mayar da hankali kan daƙile yaɗuwar yaƙi da inganta zaman lafiya a faɗin duniya.
Da yake jawabi daga fadar White House a ranar 19 ga Fabrairu, 2026, Trump ya bayyana tallafin a matsayin mafi girman gudunmawar kuɗi da mutum ɗaya ya taba bayarwa domin zaman lafiya a tarihin duniya.
Ya ce shirin ya zo ne a matsayin martani ga abin da ya kira “zagaye mara ƙarewa na rikice-rikice da barna” da suka mamaye ƙarni na 21.
A cewarsa, sabuwar cibiyar za ta kasance tamkar inshora ce ta hana barkewar Yaƙin Duniya na Uku.
Ya jaddada cewa idan ana iya kashe tiriliyoyin daloli wajen yaƙi, to ya kamata a iya ware biliyoyin daloli domin hana shi faruwa tun kafin lokaci ya ƙure. Ya ƙara da cewa manufarsa ita ce “zaman lafiya ta hanyar ƙarfi, amma kuma ta hanyar saka jari cikin hikima.”
Takardar bayani da fadar White House ta fitar ta nuna cewa “Board of Peace” za ta kasance kungiya mai zaman kanta, ba ta gwamnati ba, wadda za ta kunshi kwamitin mambobi 15 daga sassa daban-daban na duniya, ciki har da tsoffin shugabannin kasa, hafsoshin soja masu ritaya, wadanda suka taba lashe lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel, shugabannin kasuwanci, malamai da kwararru a fannin warware rikice-rikice. Duk da haka, ba a fitar da sunayen mambobin ba tukuna.
An tsara dala biliyan 10 din a matsayin asusun jari na dogon lokaci, inda za a zuba kudin cikin hanyoyin zuba jari masu aminci domin samar da kudin tafiyar da ayyukan cibiyar a nan gaba.
Trump ya bayyana cewa za a nemi ƙarin gudunmawa daga kamfanoni da masu hannu da shuni, amma ya nace cewa cibiyar ba za ta dogara da kuɗin gwamnati ba, domin ta kasance mai ’yanci daga tasirin siyasa.
Wannan sanarwa ta zo ne a daidai lokacin da duniya ke fama da rikice-rikice a yankuna daban-daban, ciki har da yakin Ukraine, tashin hankali a Gabas ta Tsakiya, da rikice-rikice a Sudan da yankin Sahel.
Trump ya sha bayyana kansa a matsayin mai iya kulla yarjejeniyar zaman lafiya, yana mai cewa a wa’adinsa na farko ya taimaka wajen hana barkewar manyan rikice-rikice na duniya.
Har yanzu ba a bayyana cikakkun bayanai kan lokacin kaddamar da shirin ba, ko inda za a kafa hedikwatarsa, duk da cewa ana hasashen za ta kasance a Florida ko wani yanki na Gabas ta Tsakiya. Ana sa ran za a ƙaddamar da cibiyar a hukumance cikin watanni biyu zuwa uku masu zuwa.

No comments