Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta yaba da tsarin zaben da ya samar da ɗan jam’iyyar YPP, Muka’il Abubakar, a matsayin Shugaban...
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta yaba da tsarin zaben da ya samar da ɗan jam’iyyar YPP, Muka’il Abubakar, a matsayin Shugaban Ƙungiyar Jam’iyyun Siyasa ta Jihar Kaduna, wato Inter-Party Advisory Council (IPAC).
A zaben da aka gudanar a ranar Alhamis, Muka’il Abubakar ya samu ƙuri’u 11 cikin 19, inda ya kayar da abokan takararsa da tazara mai yawa, domin komawa kujerar shugabancin IPAC na reshen jihar Kaduna.
Haka kuma, Musa Muhammed na jam’iyyar AAC ya zama Sakataren Ƙungiyar na Kaduna bayan nasarar da ya samu a nasa bangaren.
Da yake jawabi jim kaɗan bayan kammala zaben, Shugaban Sashen Ayyukan Zabe na INEC, Mohammed Ismail, ya bayyana cewa tsarin zaben ya kasance cike da gaskiya, tsafta da kuma nuna kamun kai ta siyasa.
Ya ce abin da ya gani ya wuce zato, domin ba a samu hayaniya ko sabani mai tsanani ba kamar yadda ake gani a wasu zabubbuka.
A cewarsa, “Tsarin ya kasance cikin natsuwa da bin ƙa’ida. A mafi yawan lokuta, zabubbuka ba sa wucewa ba tare da ƙorafi ko jayayya ba, amma a nan komai ya gudana cikin kwanciyar hankali. Wannan abin a yaba ne.”
Ya kuma jinjinawa kwamitin zaben na IPAC bisa kyakkyawan aikin da suka yi wajen tabbatar da gaskiya da adalci.
INEC ta buƙaci sabbin shugabannin IPAC a Kaduna da su yi aiki bisa dokoki da ƙa’idojin ƙungiyar, tare da tabbatar da haɗin kai tsakanin jam’iyyun siyasa domin ƙarfafa dimokurafiyya a jihar.
A nasa bangaren, sabon shugaban IPAC, Muka’il Abubakar, ya yi alƙawarin jagoranci mai ma’ana da gaskiya. Ya tabbatar wa mambobin ƙungiyar cewa ba zai ci amanar amincewar da suka ba shi ba, yana mai cewa wannan nasara ta kowa ce, ba tasa kaɗai ba.
Shugaban Kwamitin Zabe, Bashir Bala, ya taya sabbin shugabannin murna, tare da jan hankalinsu da su kiyaye dokoki da ƙa’idojin IPAC domin ci gaban siyasar jihar.
Sauran waɗanda aka zaba sun haɗa da Solomon Ayock na ADP a matsayin Mataimakin Shugaba, Fatima Sani na PDP a matsayin Mataimakiyar Sakatare, Jemilu Muhammed na jam'iyyar Accord Party a matsayin Sakataren Kuɗi, da Hassan Saleh na APP a matsayin Ma’aji. Haka kuma, Aisha Umar Faruq na BOOT Party ta zama Sakatariyar Tsare-tsare, Yusuf Shuaibu na PRP ya zama Jami’in Hulɗa da Jama’a, yayin da Hassan Subaru na NNPP ya karbi muƙamin Lauya na IPAC.

No comments