Daga Ibrahim Muhammad, Kano Shugaban al'ummar Marghi mazauna jihar Kano, Wadzani Adamu ya miƙa saƙon jajen sa ga Gwamnatin Jihar Kano ƙ...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Shugaban al'ummar Marghi mazauna jihar Kano, Wadzani Adamu ya miƙa saƙon jajen sa ga Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf da Sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi da 'yan kasuwar Kano bisa ibtila'in gobara da ya shafi 'yan kasuwar Singa.
Sarkin ya bayyana gobarar da cewa wata jarrabawa ce daga Allah, inda ya yaba da irin damuwa da ɗaukin da Gwamnatin jihar Kano da shugaban ƙasa suka nuna, tare da kawo ɗaukin tallafa wa waɗanda gobarar ta jawo musu asarar ɗimbin dukiya.
Daga nan ya yi addu'ar Allah ya kare faruwar irin wannan a nan gaba, ya kuma mayar masu da alheri, ya bunƙasa dukiyar su.
Wadzani Adamu ya kuma yi kira ga al'ummar jihar Kano da na ƙasa baki ɗaya, musamman masu hali, su tallafa wa 'yan kasuwar don ci gaba da kasuwancin su.
A ƙarshe, Sarkin na Margunawa na Kano, Wadzani Adamu ya taya al'ummar musulmi murna da shigowar watan Azumin Ramadan, tare da yin kira gare su da su kiyaye dukkan abin da Allah ya hana, kuma su yi amfani da wannan watan wajen kyautata ibada da kuma yi wa ƙasar nan addu'a ta neman zaman lafiya, kwanciyar hankali da bunƙasar arziki.

No comments