Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

BARAZANAR AMURKA: Iran Ta Aike Wa Majalisar Ɗinkin Duniya Zazzafar Wasiƙa

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta aika wata zazzafar wasiƙa zuwa ga Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres, da kuma Shugab...


Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta aika wata zazzafar wasiƙa zuwa ga Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres, da kuma Shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar, James Kariuki, tana mai yin ƙorafi kan abin da ta kira 'ci gaba da barazanar amfani da ƙarfi daga Amurka a kanta'.

A wasiƙar da Babban Jakadan Iran a Majalisar Ɗinkin Duniya, Amir Saed Iravani, ya rattaba wa hannu, gwamnatin Iran ta ce barazanar da jami’an Amurka ke yi, musamman kalaman shugaban ƙasar, sun saba wa Kundin Tsarin Mulkin Majalisar Ɗinkin Duniya da dokokin ƙasa da ƙasa.

Iran ta yi nuni da wani saƙo da Shugaban Amurka ya wallafa a shafukan sada zumunta a ranar 18 ga Fabrairu, 2026, inda ya yi ishara da yiwuwar amfani da sansanin soji na Diego Garcia da kuma filin jirgin sama na Fairford domin kai farmaki kan Iran idan har ba a cimma wata yarjejeniya ba.

A cewar Iran, irin waɗannan kalamai ba za a ɗauke su a matsayin barkwanci ko furuci na siyasa kawai ba, musamman a lokacin da ake ganin ana ci gaba da tara kayan yaƙi da rundunonin soji a yankin. Ta ce hakan na iya jefa yankin cikin sabon rikici mai muni, wanda zai iya kawo cikas ga zaman lafiya da tsaron duniya baki ɗaya.

Sai dai Iran ta jaddada cewa har yanzu tana biyayya ga manufofi da ƙa’idojin Majalisar Ɗinkin Duniya, tare da nuna cewa tana da niyyar warware sabani ta hanyar diflomasiyya. Ta ce tana ci gaba da tattaunawar nukiliya da Amurka cikin gaskiya da kishi, domin a ɗage takunkuman da ta kira "na zalunci" da aka ƙaƙaba mata, tare da warware duk wata shakka game da shirinta na nukiliya wanda ta ce na zaman lafiya ne kawai.

Iran ta bayyana cewa idan Amurka ta shiga tattaunawar da cikakkiyar niyya da mutunta dokokin ƙasa da ƙasa, zai yiwu a cimma matsaya mai ɗorewa wadda za ta mutunta haƙƙoƙin ƙasashe mambobin yarjejeniyar hana yaɗuwar makaman nukiliya (NPT).

A ƙ

 

Iran ta yi kira ga Kwamitin Tsaro da Babban Sakataren Majalisar da su yi amfani da ikon da Kundin Tsarin Mulki ya ba su wajen tabbatar da cewa Amurka ta dakatar da duk wata barazanar amfani da ƙarfi, musamman bisa tanadin Sashe na 2(4) na kundin, wanda ya haramta barazanar ko amfani da ƙarfi a kan wata ƙasa mai cikakken iko.

Daga nan ta yi gargaɗi cewa idan aka bar irin wɗannan barazana ba tare da ɗaukar mataki ba, hakan na iya zama wata al’ada a harkokin siyasa ta duniya, lamarin da zai iya jefa kowace ƙasa cikin haɗari a nan gaba.

Amma duk da haka, Iran yi gargaɗi, tare da sake jaddada cewa ba ta neman rikici ko yaƙi, kuma ba za ta fara yaƙi ba, amma idan aka kai mata farmaki, to za ta yi amfani da haƙƙin ta na kare kai, kamar yadda Sashe na 51 na Kundin Majalisar Ɗinkin Duniya ya tanada.

A irin wannan yanayi, Iran ta ce in abin ya kai ga an kai mata, to duk wani sansani, kayan aiki ko kadarorin rundunar da ta kai mata hari a yankin za su zama halastattun wuraren kai farmaki a martaninta na kare kai, tare da ɗora wa Amurka alhakin duk wata illa da za ta biyo baya.

Iran ta ce, in har aka yi gigin kai mara, to la budda za ta kare kanta, za ta mayar da martani mai gauni, wanda zai girgiza duniya baki ɗaya, inda Amurka za ta fi ɗanɗana kuɗa.

Jakadan ya buƙaci a rarraba wasiƙar a matsayin takarda ta hukuma ta Kwamitin Tsaro.

No comments