Hafsoshin Sojin Nijeriya aƙalla 16 ne za su fuskanci hukuncin kisa ko ɗaurin rai-da-rai bisa laifin yunƙurin hamɓarar da gwamnatin Shugaban ...
Hafsoshin Sojin Nijeriya aƙalla 16 ne za su fuskanci hukuncin kisa ko ɗaurin rai-da-rai bisa laifin yunƙurin hamɓarar da gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Rundunar Sojin Nijeriya ta sanar da cewa binciken da ta kammala bayan tsare waɗanda ake zargin ya same su da laifin yunƙurin kifar da gwamnati.
Wasu tsofaffin Hafsoshin sojin Nijeriya sun bayyana cewa hukuncin kisa shi ne abin da dokar aikin sojin ƙasar ta tanada kan duk wanda aka samu da hannu a yunƙurin juyin mulki.
A watan Oktoban bara ne rahoto ya ɓulla cewa Rundunar Sojin Nijeriya, ta hannun Hukumar Binciken Leƙen Asiri ta Soji (DIA) ta tsare wasu hafsoshinta 16 masu muƙamin Kyaftin zuwa Birgediya-Janar kan zargin yunƙurin yi wa Shugaba Tinubu juyin mulki.
An ruwaito a ranar Litinin cewa kwamitin da rundunar ta kafa ya kammala bincikensa tare da miƙa rahotonsa ga Shugaba Tinubu domin ɗaukar mataki na gaba.
Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya, Manjo-Janar Samaila Uba, ya tabbatar cewa kwamitin ya miƙa rahotonsa ga “mahukuntan da suka dace.”
Sanarwar da Manjo-Janar Samaila Uba ya fitar a ranar Litinin ta ce za a gurfanar da waɗanda aka samu da laifi a gaban kotun soji domin yanke musu hukuncin da dokokin aikin soji suka tanadar.
Ya ce, “Rundunar Sojin Nijeriya tana sanar da al’umma cewa an kammala binciken tare da gabatar da rahoton ga mahukunta da suka dace kamar yadda doka ta tanadar.
“An kammala zuzzurfa kuma cikakken bincike kan duk waɗanda ake zargin, bisa tanadin dokokin aikin soji.
“Binciken ya gano cewa daga a cikin waɗanda ake zargi da hannu a yunƙurin hamɓarar da gwamnati, wanda yin hakan ya saɓa wa tsarin aikin sojin Najeriya; don haka za a gurfanar da su a gaban kotun soji da sauran dokokin ƙasa.”
Ya bayyana cewa an sanar da jama’a halin da ake ciki ne domin komai ya kasance a fili da kuma tabbatar da adalci, a yayin da rundunar za ta kiyaye ƙa’idojin aikinta cikin ƙwarewa, da kuma biyayya da kare dokar ƙasa.
Ya ce doka ce ta tanadar da matakan ladabtarwa da aka ɗauka domin tabbatar da ɗa’a da kuma ƙwarewa a tsakanin jami’an rundunar.

No comments