Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Barci A Bakin Aiki Ya Sa An Kwace Lasisin Ma'aikaciyar Jinya ’Yar Nijeriya A Australia

Hukumar Kula da Ma’aikatan Jinya a jihar New South Wales ta ƙasar Australia ta soke lasisin wata ’yar asalin Nijeriya mai suna Chimzuruoke O...




Hukumar Kula da Ma’aikatan Jinya a jihar New South Wales ta ƙasar Australia ta soke lasisin wata ’yar asalin Nijeriya mai suna Chimzuruoke Okembunachi, bayan wata kotu ta gano cewa ta riƙa yin barci yayin da take bakin aiki a wani gidan kula da tsofaffi da ke birnin Sydney.

Kotun ta bayyana cewa halayen nata sun kai matsayin rashin kwarewar aiki mai tsanani, lamarin da ya iya jefa rayuwar marasa lafiya cikin haɗari.

A cewar hukuncin, matar mai shekaru 25 ta kasance ita kaɗai ce ma’aikaciyar jinya mai rijista da ke kula da tsofaffi kusan 100 a lokacin da take aikin dare.

Rahotanni sun nuna cewa ta fara aiki a cibiyar Hardi Aged Care da ke Guildford a watan Fabrairu na shekarar 2024, amma cikin ƙasa da wata guda aka dakatar da ita, kafin daga bisani ta ajiye aiki da kanta.

A cewar bayanan da kotun ta saurara, Okembunachi ta yi barci a wurin aiki sau shida a tsakanin ranakun 13 zuwa 27 ga Maris, 2024. A wasu daga cikin dararen, an ruwaito cewa wasu marasa lafiya sun rasa shan magungunan rage raɗaɗi na morphine da aka tsara musu, sakamakon rashin kulawa yadda ya kamata.

Binciken ya kuma gano cewa ta taba umartar wata ma’aikaciyar taimako ta bai wa mara lafiya magani alhali ba ta da izinin yin hakan, abin da ya ƙara dagula matsalar marasa lafiya a cibiyar.

Abokan aikinta ne suka fara tada hankalin shugabanni kan halayenta a ranar 27 ga Maris, wanda hakan ya janyo dakatar da ita washegari.

No comments