Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sojojin Nijeriya Sun Yi Nasarar Kashe Babban Kwamandan ISWAP a Arewa Maso Gabas

Sojojin Operation Haɗin Kai sun sake samun gagarumar nasara a yaƙin da suke yi da ’yan ta’adda a Arewa maso Gabas, inda suka kashe wani babb...


Sojojin Operation Haɗin Kai sun sake samun gagarumar nasara a yaƙin da suke yi da ’yan ta’adda a Arewa maso Gabas, inda suka kashe wani babban kwamandan ISWAP mai suna Julaibib a yankin Kimba, cikin Karamar Hukumar Damboa ta Jihar Borno. 

Bayanai sun nuna cewa marigayin na daga cikin manyan jagororin da ke ta’addanci a yankin Gujba na Timbuktu Triangle, kuma kashe shi ya jefa ’yan ISWAP cikin rudani tare da raunana tsarin jagoranci da umarninsu.

A wasu hare-hare na daban, sojojin tare da haɗin gwiwar Civilian Joint Task Force sun kashe ’yan ta’adda uku a wani kwanton bauna tsakanin Ngazalgana da Lamusheri a Borno, inda suka kwato bindigogin ƙirar AK-47 guda biyu. Haka kuma, a Tsokorok da ke Karamar Hukumar Gwoza, sojoji sun fatattaki ’yan Boko Haram/ISWAP, suka kashe guda ɗaya tare da kwato babura biyu, ba tare da asara a ɓangaren sojoji ba.

A Jihar Adamawa kuwa, sojoji sun dakile yunƙurin fashi da makami a Mubi ta Arewa, inda suka kama mutane biyu da ake zargi, sannan suka kwato makamai da kayayyaki. A wani sintiri kuma, sojoji tare da ’yan sa-kai sun fafata da ’yan ta’adda a yankin Amtasa–Washim, suka ceto wata mata da aka sace tare da kwato bindigogi da harsasai. 

Rundunar Operation Hadin Kai ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da aiki tukuru domin tabbatar da tsaro da dawo da zaman lafiya a Arewa maso Gabas.
 

No comments