Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya shawarci matasan Nijeriya da su yi amfani da damarmakin da gyare-gyaren ƙas...
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya shawarci matasan Nijeriya da su yi amfani da damarmakin da gyare-gyaren ƙasa da ake aiwatarwa suke samarwa, yana mai bayyana su a matsayin muhimman hanyoyi na ci gaban kai da gina ƙasa.
Ministan ya bayyana haka ne yayin gabatar da Laccar Kammala Karatu ta shekarar 2026 a Bikin Kammala Karatu na 34 na Jami’ar Fasaha ta Tarayya, Minna, Jihar Neja. Taken laccar shi ne: “Matasa da Gina Ƙasa: Amfani da Dama a Zamanin Gyare-gyaren Ƙasa.”
Lokacin da yake jawabi ga ɗaliban da suka kammala karatun, Ministan ya bayyana Nijeriya a matsayin ƙasa ce mai yawan matasa da babbar dama, yana mai cewa makomar ƙasar ta fi dogara ne kan yadda ake ba matasa ilimi, ƙwarewa da kuma shigar da su cikin harkokin cigaban ƙasa.
Ya ce: “Nijeriya, kamar sauran ƙasashen Afrika, ƙasa ce mai matuƙar yawan matasa; rabin al’ummar mu ba su kai 'yan shekara 20 ba, yayin da kashi uku cikin huɗu ba su kai 'yan shekara 35 ba. Da ilimi nagari, horar da ƙwarewa, da shirye-shiryen fuskantar sauye-sauyen wuraren aiki na ƙarni na 21, Nijeriya za ta zama mai ƙarfi a duniya wanda ba za a iya tsayarwa ba.”
Ya ƙara da cewa gyare-gyaren da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta gabatar an yi su ne da hangen nesa kuma suna da matuƙar muhimmanci domin sake daidaita tattalin arziki da tsarin mulki na ƙasar nan, yana mai jaddada cewa ba za a iya gina ƙasa ba tare da garambawul ba.
Ya ce: “Ba a gina ƙasa ba tare da gyare-gyare ba. Gyare-gyare na kare mu daga maimaita abu ɗaya kullum tare da tsammanin sakamako daban.”
Da yake haskaka manyan gyare-gyare kamar cire tallafin man fetur, daidaita kasuwar canjin kuɗi, da sababbin dokokin haraji, Ministan ya ce manufar ba ta zama nauyi ga ’yan ƙasa ba, sai dai samar da tsari mai adalci da gaskiya wanda zai buɗe hanyoyin samun kuɗaɗe don ci gaba da zuba jari.
Ya ce: “Ba a taɓa nufin karɓar ƙari daga ’yan Nijeriya ba; a maimakon haka, ana da nufin sauƙaƙa haraji tare da mayar da shi mai adalci da gaskiya.”
Idris ya bayyana cewa gyare-gyaren sun fara jawo sabon ƙwarin gwiwar masu zuba jari tare da samar da damarmaki a fannoni da dama, ciki har da fasaha, noma, makamashi mai sabuntawa da tattalin arzikin ƙirƙira, inda matasan Nijeriya suke kan gaba wajen cin gajiyar hakan.
Ya kuma yi nuni da shirye-shiryen gwamnati irin su Asusun Rancen Ilimi na Ƙasa (NELFUND), wanda ya tallafa wa ɗaruruwan dubban ɗalibai, a matsayin hujjar cewa Ajandar Sabuwar Fata Tagari na haifar da sakamako a zahiri.
Ya ce: “Ta hanyar NELFUND, muna da tabbatacciyar hujja cewa Ajandar Sabuwar Fata Tagari gaskiya ce, tana aiki, tana da tasiri, kuma tana sauya rayuwa.”
A ƙarshe, Ministan ya ƙarfafa gwiwar waɗanda suka kammala karatu da su ɗauki kan su a matsayin masu gina ƙasa, yana mai kira gare su da su rungumi damarmaki, su bunƙasa ƙwarewar su, su rungumi koyon ilimi har tsawon rayuwa, tare da la’akari da aikin gwamnati a matsayin wata hanya ta bayar da gudunmawa ga ƙasa.
Ya ce: “Za ku iya gina ƙasa daga inda kuke, da abin da kuke da shi. Ba sai kun tara dukiya ko tasiri sosai ba kafin ku ba da gudunmawa. Ku fara tun yanzu.”
Ministan ya taya ɗaliban da suka kammala karatu murna, tare da gode wa shugabannin Jami’ar Fasaha ta Tarayya, Minna, bisa gayyatar sa don gabatar da Laccar Kammala Karatu.
Daga cikin manyan baƙin da suka halarta akwai wakilin Gwamnan Jihar Neja, Mista Obet Nana, wanda shi ne Kwamishinan Yaɗa Labarai; Mataimakin Shugaban Jami’a (Vice Chancellor) na FUT Minna, Farfesa Abdallah Adamu Kuta; tsohon VC na FUT Minna, Muftau Akanji; Sanata Peter Nda Alkali mai wakiltar Yankin Sanatan Neja na Kudu; Darakta Janar na gidan rediyon Muryar Nijeriya (VON), Malam Jibrin Baba Ndace; tsohon Ministan Wasanni, Alhaji Sani Ndanusa, da sauran manyan baƙi masu daraja.









No comments