Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

BARIN ALMAKASHIN TIYATA A CIKI: Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Wasu Ma’aikatan Lafiya

Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Kano ta tabbatar da cewa lamarin mutuwar Aishatu Umar, wacce ta rasu sakamakon barin Almakashi a cikin ta...


Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Kano ta tabbatar da cewa lamarin mutuwar Aishatu Umar, wacce ta rasu sakamakon barin Almakashi a cikin ta bayan yi mata aikin tiyata, ya faru ne a cibiyar lafiya ta Abubakar Imam Urology Centre, inda ta yi zargin sakacin likitoci ne ya janyo haka.

A cikin wata sanarwa da jami’ar hulɗa da jama’a ta hukumar, Samira Suleiman, ta fitar a daren Talata, hukumar ta ce binciken farko da babban sakataren ta, Dakta Mansur Mudi Nagoda, ya bayar da umarni, ya tabbatar da cewa “lamarin baƙin ciki da ya shafi marigayiya Aishatu Umar ya faru a cibiyar Abubakar Imam Urology Centre.”

Sanarwar ta ce, bisa ƙudirin hukumar na tabbatar da ɗaukar alhaki, “an dakatar da ma’aikata uku da ke da hannu kai tsaye a lamarin daga duk wani aikin jinya nan take.”

Hukumar ta ƙara da cewa, an miƙa lamarin ga Kwamitin Ƙa’idojin Ɗabi’a na Likitoci na Jihar Kano domin ci gaba da bincike da ɗaukar matakin ladabtarwa idan ya dace.

A cewar hukumar, hakan zai tabbatar da “ɗaukar matakin ladabtarwa da ya dace bisa dokoki, ƙa’idoji da kuma ɗabi’a.”

In dai ba a manta ba, wannan lamari ya faru ne ga wata mata mai ’ya’ya biyar, Aishatu Umar, wacce ta rasu a jihar Kano sakamakon abin da iyalanta ke zargi a matsayin sakacin likitoci a asibitin Abubakar Imam Urology Centre, inda aka ce an bar mata kayan aikin tiyata a cikin jikinta bayan an yi mata aiki a watan Satumba.

Rasuwar ta ta zo ne ƙasa da mako guda bayan rahoton mutuwar wani yaro ɗan marubuciya Chimamanda Adichie, wanda aka ce ya faru sakamakon sakaci a bangaren kiwon lafiya, lamarin da ya ƙara hura wutar fushi da kira ga ɗaukar mataki kan ingancin tsarin kiwon lafiya a ƙasar.

Rahotanni sun ce Aishatu ta rasu da misalin ƙarfe 1:00 na dare a ranar Talata, bayan shafe watanni tana fama da matsanancin ciwon ciki bayan an yi mata tiyata, wadda a farko aka ce za ta taimaka wajen inganta lafiyarta. Maimakon haka, halin nata ya ta’azzara, har ya kai ga mutuwarta.

Da yake magana a madadin iyalan marigayiyar, Abubakar Mohammed ya ce Aishatu ta kamu da rashin lafiya ne watanni da suka gabata, inda aka kwantar da ita a cibiyar urology domin yi mata tiyata. Ya bayyana cewa bayan kammala aikin, matsaloli suka biyo baya, inda ta fara fama da ciwon ciki mai tsanani da ke dawowa akai-akai.

A cewarsa, marigayiyar ta riƙa komawa asibitin tsawon kusan watanni huɗu tana ƙorafin halin da take ciki, amma sai ma’aikatan lafiya suka rinƙa ba ta magungunan rage raɗaɗi kawai, ba tare da yin cikakken bincike don gano musabbabin matsalar ba.

Iyalan sun ƙara da cewa kwanaki biyu kacal kafin rasuwarta ne aka yi mata cikakken gwaji, ciki har da hotunan na’ura, inda aka gano cewa an bar almakashi na tiyata a cikin jikinta tun lokacin aikin da aka yi mata a watan Satumba.

Bayan wannan ganowa, an ce ana shirin sake yi mata wani aikin gyara, amma halin nata ya ƙara tsananta cikin gaggawa kafin a kai ga yi mata aikin, lamarin da ya kai ga mutuwarta.

Iyalan sun bayyana wannan lamari a matsayin mummunan tauye ƙa’idojin aikin likitanci da tsaron marasa lafiya, tare da kiran gwamnatin jihar Kano da hukumomin da ke kula da harkokin lafiya da su gudanar da bincike mai zurfi domin tabbatar da an yi adalci.
 

No comments