Daga Khalid Idris Doya Marigayi Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi ya bayyana cewar bayan ya rasuwar sa bai amince ba, kuma bai yarda a ware rana t...
Marigayi Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi ya bayyana cewar bayan ya rasuwar sa bai amince ba, kuma bai yarda a ware rana ta musamman a ranar 2 ga watan Al-Muharram domin yin Mauludin tunawa da ranar haihuwar sa ba.
Marigayin ya bayyana haka ne daga cikin wasiyyar da ya bayar. Cikin tawali'u da ƙanƙan da kai, Marigayin ya ce, shi bai kai wanda za a rinƙa gudanar da Maulidin tunawa da shi ba, kamar yadda ake yi wa Manzon Rahama, su Shehu Tijjani da Shehu Ibrahim Inyass.
Marigayin, wanda ya rasu a ranar Alhamis ya bayyana cewar shi kawai Muƙaddami ne daga cikin Muƙaddaman Shehu, kuma hadimin sa, sannan surukin sa, inda ya bayyana cewa hakan ma kawai ya ishe sa alfahari.
Shehu Ɗahiru Bauchi ya nuna cewa idan har an ce kowane Muƙaddamin Shehu za a rinƙa yi masa Maulidin tunawa da shi, to kowace rana ma za ta zama ta gudanar da maulidodi ne domin yawan Muƙaddaman da ake da su.
Ya bayyana da bakin sa cewa: "Amma ni ban yarda a ce wata rana za a yi taro yau 2 ga watan Muharram ranar da aka haifi Shehu Ɗahiru muke yin Maulidi, ban yarda ba, kada a yi min bayan rayuwa ta.
"Amma na ji wani yana cewa Rabi'ul Auwal ya ƙunso mana (ya zo mana) da Annabi Muhammadu (SAW), Safar ya ƙunso mana Shehu Tijjani (R), Rajab ya ƙunso mana Shehu Ibrahim (R), ya ce wai Muharram ya ƙunso musu Shehu DLƊahiru. To wannan kada a sake faɗa, kada na sake ji.
"Ni ba kowa ba ne cikin wannan tsarin ni Muƙaddami ne. Ni Muƙaddami ne daga cikin muƙaddaman Shehu. Yanzu kowani Muƙaddamin Shehu sai an masa Maulidi ranar haihuwarsa nawa kenan? akwai ranar da za ta wuce ba a samu Maulidi ba?
"In an ce kowani Muƙaddamin Shehu za a masa Maulidi akwai ranar da ba Maulidi ke nan a Nijeriya? To ban yarda kada a sa sunana a cikin waɗanda ake ma wannan abu," in ji shi.
Ya sake fayyace wasiyyar tasa da cewa, "Kuma ko na mutu kada a ce yau ranar biyu ga watan Muharram za a yi Maulidin Shehu Ɗahiru, ban yarda ba, ban yarda ba; A bar ni kamar sauran 'yan uwana Mukaddamai."
Ya sake nanata cewa shi "Ni ba kowa ba ne illa muƙaddami cikin Muƙaddaman Shehu, kuma wannan ya isheni alfahari, hadimin sa kuma surukin sa, Alhamdillahi."
A gefe guda ya ce Maulidin tunawa da Shehu Ibrahim da ake yi a watan Rajab shi ne ya fara gudanar.

No comments